An Kaddamar Da Kamfe Na Zaben Raba Gardama A Chadi
A yau ne aka fara kamfe na zaben raba gardama kan garambawul a kudin tsarin mulkin kasar Chadi. An soma kamfe na musamman domin gudanar da kuri’a kan sabon kundin tsarin mulki a kasar, wanda ake ganin hakan zai iya zama zakaran gwajin dafi ga gwamnatin mulkin sojin kasar da kuma zuri’ar Itno da ta […]
Falasdinawa Suna Murnar Sako Mata 39 Ta Hanyar Musayar Fursunoni ,
Musayar fursunonin da aka yi a jiya Juma’a a tsakanin HKI da kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hmas, an sako matan Falasdinawa 39 daga kurkuku. Sakin fursunonin na jiya shi ne zango na farko a tsarin da aka yi a karkashin tsagaita wuta da zai dauki kwanaki 4. Daga cikin wadanda aka saki din a […]
Yarjejeniyar tsagaita wuta a zirin Gaza ta fara aiki a hukumance
Da karfe 7 na safiyar yau Juma’a 24 ga wata bisa agogon wurin, yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin kungiyar Hamas da Isra’ila a zirin Gaza ta fara aiki a hukumance. ©Cri
Za a dawo da ’yan Najeriya dake gudun hijira a kasashen Kamaru da Chadi da Janhuriyyar Nijar zuwa garuruwan su
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce, shirye-shirye sun kan kama wajen fara debo ’yan Najeriya da suke gudun hijira a kasashen Kamaru da Chadi da kuma Jamhuriyyar Nijar zuwa garuruwansu. Kwamishinan tarayyar a hukumar lura da ’yan gudun hijira da mutanen da suka yi kaura daga gidajensu sakamakon rikice-rikicen cikin gida Alhaji Ahmed Tijjani ne […]
An kaddamar da helkwatar shiyya ta MDD a Senegal
Shugaban kasar Senegal Macky Sall, ya jagoranci kaddamar da helkwatar shiyya ta MDD a birnin Diamniadio mai nisan kilomita 30 daga Dakar, fadar mulkin kasar. Ofishin wanda aka kaddamar a jiya Alhamis, zai zamo mazaunin hukumomi 34 na MDDr dake Senegal. Kaza lika taron kaddamarwar ya samu halartar mataimakiyar sakatare janar na MDD Amina Mohammed, […]
Fiye Da Makamai Masu Linzami 50 Hizbullah Ta Harba Akan Sansanonin Israila
Kafafen watsa labarun israila sun ce da’irar da Hizbullah take kai wa hari da makamai masu linzami ta kara fadada a wannan Alhamis. Mai Magana da yawun sojojin mamaya na israila ya ce; Abinda yake faruwa akan iyakar Arewa yana nuni da kara tabarbarewar al’amurra, sannan kuma zai iya karuwa.” Kafafen watsa labarun Israila […]
Kisan Mata Da Kananan Yara Babbar Gazawa Ce Ga Isra’ila A Yakinta Kan Gaza
Shugaba Ibrahim Raeisi ya ce gwamnatin Isra’ila ta gaza cimma dukkanin manufofinta ta hanyar kaddamar da yakin da take yi kan al’ummar zirin Gaza. Shugaban na Iran ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a birnin Tehran a yammacin jiya Laraba, tare da wakilan wasu gidajen talabijin na harshen Larabci […]
Hizbullah Tana Jana’izar Shahidai 5 A Yau Alhamis
A wannan Alhamis din an yi jana’izar shahidai biyar a garuruwa mabanbanta na kudancin Lebanon. A garin Hula na yi jana’izar Shahid Ahmad Hassan Mustafa, sai kuma shahid Muhammad Hassan Ahmad Shari wanda aka yi tashi janazar a Kharbat-Salam. A can yankin Biqa’a kuwa an yi janazar Muhammad Rabi’ah Audah, a garin al-khadra. Sai […]
Daraktan Makabartar Sojojin Isra’ila: “Mun Binne Sojoji 50 Da Aka Kashe A Gaza Cikin Sa’o’i 48
Daraktan makabartar sojoji ta Mount Herzl ya bayyana dimbin sojojin Isra’ila da aka binne sakamakon yakin da suke yi a zirin Gaza, inda aka binne sojoji 50 cikin sa’o’i 48. David Oren Baruch, daraktan makabartar sojoji ta Mount Herzl, ya ce: “Yanzu muna cikin wani lokaci da a kowace sa’a ana yin jana’izar soja […]
Najeriya: Farashin Man Fetur Ya Kara Hawa Zuwa Naira N630.63 A Cikin Watan Octoban Da Ya Gabata
Hukumar kididdiga ta kara a tarayyar Najeriya ta bada sanarwan cewa a cikin watan Octoban da ya gabata farashin man fetur ya karo a kasar zuwa naira 630.63 kan ko wace lita daga naira 195.29 a farkon wannan shekara. Hukumar ta kara da cewa tana sanya ido a kan yadda farashin man yake jujjuyawa […]