Ahlul Baiti

Jaridar Isar da Sakon Jikokin Manzon Allah (S.A.W)

Month: February 2023

February 27, 2023

Gwamna Lalong ya fadi zaben Sanatan Filato ta Kudu

  Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong na jam’iyyar APC, wanda shi ne Daraktan yakin neman zaben shugaban kasa na APC, ya sha kaye a zaben Sanatan Filato ta Kudu. AVM Napoleon Bali (mai ritaya) na jam’iyyar PDP ne, ya lashe zaben. Dan takarar na jam’iyyar PDP Napoleon Bali, ya kayar da gwamna Lalong na jam’iyyar […]

February 27, 2023

Gwamnan Benuwe ya fadi takarar kujerar Sanata

Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benuwe, ya sha kaye a yunkurinsa na lashe kujerar Sanatan Benuwe ta Arewa maso Yamma. Dan takarar jam’iyyar APC, Cif Titus Zam ne ya lika shi da kasa a zaben. Babban jami’in zaben, Farfesa Rufus Shaato ya bayyana Zam a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar Benuwe ta Arewa Maso […]

February 27, 2023

Shugaban majalisa Ahmed Lawan ya lashe zaben Sanatan Yobe-ta-Arewa

  Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan na jam’iyyar All Progressives Congress, APC, ya lashe zaben Sanatan Yobe-ta-Arewa a Yobe. Da ya ke bayyana sakamakon zaben a Gashua a yau Litinin, jami’in zaben, Farfesa Omolala Aduoju na jami’ar tarayya, Gashua, ya ce Lawan ya samu kuri’u dubu 91,318. “Bayan cika sharuddan doka kuma ya samu mafi […]

February 27, 2023

Dan gidan gwamnan jihar Kano Umar Abdullahi Umar, ya faɗi zaɓen dan takarar majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Tofa da Rimin Gado. Hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ce ta bayyana sakamakon ranar Lahadi. Dan takarar jam’iyyar NNPP Tijjani Jobe ne ya samu nasara da ƙuri’u 52,456, inda shi kuma Umar ganduje ya […]

February 27, 2023

Ankarbi sakamakon zaben jihohi Hudu.

A hukumance kawo yanzu, shugaban hukumar zaɓen Najeriya INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya karɓi sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na jihohi huɗu. Jihohi huɗun da aka gabatar da sakamakonsu a zauren taron sun haɗar da Ekiti da Kwara da Osun da kuma Ondo. Sakamakon dai ya nuna dan takarar jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya samu […]

February 27, 2023

Danjuma Goje ya sake lashe zaben Sanata karo na 4 a Gombe

Tsohon Gwamnan Jihar Gombe, Danjuma Goje, ya sake lashe zaben Sanatan Gombe ta Tsakiya a karo na shida a jam’iyyar APC. Goje ya lashe zaben ne da kuri’a 102,916, inda ya doke babban abokin hamayyarsa na PDP, Aliyu Abubakar wanda ya sami kuri’a 37,970 Daga Haruna Gimba Yaya, Gombe da Sani Ibrahim Paki

You are here: Page 1