Ahlul Baiti

Jaridar Isar da Sakon Jikokin Manzon Allah (S.A.W)

July 28, 2021

ME YA SA ‘YAN SHI’A SUKE SUJADA AKAN TURBA?

ME YA SA ‘YAN SHI’A SUKE SUJADA AKAN TURBA?

“Turba” kalma ce ta larabci wanda yake nufin “K’asa”. ‘yan shia suna sallah a kan kasa ne saboda abinda yazo a fikhu na wajabcin yin sujada a kan kasan, da rashin ingancin yin sujada a kan wani abunda ba kasan ba saidai in shima dangin kasan ne kamar dutse da makamancin sa, ko kuma abinda ya fito daga kasan na tsirrai, saidai abinda bai hallata ba a yi akan sa sune abinda yake abinci ne ko tufafi. yin sujada akan koma bayan wadannan abubuwan da aka sharadanta yana sanya rashin ingancin sallah wanda yake shine ibada mai daraja ta daya a muhimmanci.
Da wannan ne yasa ‘yan shia domin saukakawa suke kwaba laka su busar da shi suna yin sujadan a kan sa. Wannan shi ya haifar da za ka taras ‘yan shia suna daukan wannan turba a tare dasu domin idan sallah ya same su saisu sanya domin yin sujada a kan sa musamman idan wajen sallar ko masallacin a shimfide yake da shinfidu na zamani, haka ma shi ya sanya in ka shiga masallatan ‘yan shia zaka tarar da wadannan dunkulallun kasa wanda ake kira turba domin a rika sanya goshi ana sujada akan sa sakamakon masallatai shinfide suke da shinfidu na zamani

HADISAN AHLUSSUNNA WADANDA SUKA NUNA WAJABCIN YIN SUJADA AKAN K’ASA

Duk da cewa malaman Ahlus sunna sun halatta yin sujada akan komai to amma akwai hadisai suma a cikin litattafan ruwayoyin su wadanda suka nuna cewa sujada baya inganta sai aka kasa.

 1. Yazo a cikin Sahihiul Bukhari, Manzon Allah s.a.w.a yace ‘’An sanya kasa gare ni ya zamo abin sujada da tsarkakewa.(Sahihul Bukhariy juzu’i na 1 shafi na 91, sunanu Baihakiy juzu’i na 2 shafi na 433 da sauran litattafan ruwayoyi).
 2. Yazo cikin Musnad na Ahmad bin Hanbal daga Ummulmu’uminina Maimuna tace manzon Alla S.A.W.A ya kasance yana sujada akan yankin tabarmar da aka saka da ganye dabino. (musnad Ahmad bin Hanbal juzu’i na6 shafi 331).

 

 1. Yazo cikin Musannaf na Ibn Abu Shaiba, daga Ummul muminina A’isha tace ban taba ganin Mazon Allah ya dora goshin sa akan wani abu ba (koma bayan kasa) (musannaf juzu’i na 1 shafi na397).

 

 1. An rawaito hadisi daga daga Wa’il bin Hujur yana cewa “lallai Annabi S.A.W.A idan zaiyi sujada yakan sanya goshin sa da hancin sa akan kasa ne. (Musnad Ahmad bin Hanbal juzu’i na 1 shafi na 315).

 

Sahabban Manzon Allah suma sun kasance basa yin sujada akan wani abu face ka kasa koda kuwa a cikin yanayi mai wahala ne.

5. An samo hadisi daga Jabir bin Abdullahil Ansariy yana cewa na kasance ina sallah tare da Annabi s.a.w.a sallar azahar (a lokacin tsanin zafi), sai na kwashi damki na kasa, sai na sanya shi a hannu na ina juyawa zuwa wani hannu saboda tsananin zafi har sai da yayi sanyi sannan sai na saka shi a goshi na ina sujada a kan sa.

Bayan hakaito wannan hadisi baihakiy yayi ta’aliki yace da ace ya halatta ayi sujada akan tufafi wanda yake tare dashi a jikin sa, da yafi sauki yayi akan tufan maimakon (ya sha wahala wajen) sanyaya kasa.

 1. An karbo hadisi daga Ibn Abbas cewa Manzon Allah yana sujada akan dutse (Sunanu Baihakiy; juzu’i na 2 shafi na102).
 2. A cikin littafin Musannaf an ruwaito daga sahabin Ibn Mas’ud yana cewa, shi Ibn Mas’ud din baya sujada akan wani abu in ba kan kasa ba koda kuwa a cikin jirgin ruwa ne sai ya riki wani yanki daga kasa ya hau da shi domin yayi sujada a kan sa. (musannaf juzu’i na 1 shafi na 367)

Akwai ruwayoyi masu yawa wanda suke nuna wajabci da muhimmancin yin sujada akan kasa. Mai neman zurfafa bincike yana iya duba littafin Silsilatul Masa’ilil Fiqihiyya, mas’ala ta shida na Shaikh Allama Ja’afarus Subhaniy.

 

 

Daga:

Mallam Murtala Isa Dass

SHARE:
Makala 2 Replies to “ME YA SA ‘YAN SHI’A SUKE SUJADA AKAN TURBA?”
Ahlul Baiti
Ahlul Baiti

COMMENTS

2 thoughts on “ME YA SA ‘YAN SHI’A SUKE SUJADA AKAN TURBA?

  Author’s gravatar

  Allah yasaka da alkairi.
  .Dan Allah inada tambaya ya halatta ayi sujjada akan tayal’s

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *