Ahlul Baiti

Jaridar Isar da Sakon Jikokin Manzon Allah (S.A.W)

Category: Makala

September 15, 2023

Ladan Ziyaran Ƙabarin Manzon Allah (S).

  An ruwaito daga ma’aikin Allah (S) yace: “Wanda ya ziyarci ƙabari na bayan rasuwa ta, kamar wanda yayi hijira ya dawo gareni ne a lokacin da nake raye, idan baku sami dama ba ku aiko mini da sallama, domin zata iso gareni” Attahzeb 6/3 Sheikh Tousi

September 3, 2023

SIRRIN SAMUN NASARA MATAKI NA HUDU: DAMA TA YALWAR LOKACI

DAMA TA YALWAR LOKACI Ka ribaci lokacinka kafin shagaltuwarka. Lallai dama ta yalwar lokaci ba kowa ne ya fahimce ta ba, sai ‘yan kadan daga cikin mutane, da yawa suna da yalwar lokacin da ya ishe su su yi ayyuka masu yawa, amma ba su amfana da shi ba, sai su bar abin sai nan […]

August 31, 2023

MATAKI NA HUDU AMFANI DA DAMA

Sirrin Samun Nasara Kowannenmu ya san cewa kowane abu a cikin wannan rayuwar mai karewa ne, rana tana karewa da zuwan dare, karfi yana karewa ya zama rauni, kuruciya tana komawa tsufa, mutum yana komawa kasa, dukkan wani abu da yake a wannan rayuwar yana komawa zuwa kishiyarsa. Hakika damar da mutum yake samu ba […]

August 30, 2023

SIRRINSAMUN NASARA MATAKI NA UKU YIN AIKI DA JAJIRCEWA

  SirrinSamun Nasara: Yana daga cikin abubuwa mafiya muhimmanci da suke isar da mutum zuwa ga cimma burinsa shi ne: Jajircewa a aiki. Idan ka lura da abin da ke gudana a tsakanin halittu da abin da ke gudana tare da su, za ka fahimci wata hakika ta cewa dukkan wani samamme yana bayyanar da […]

August 28, 2023

KA’IDA TA FARKO MECE CE NASARA?

Kowane mutum a wannan rayuwar yana son ya yi nasara ya samu farin ciki, yana burin ya samu nasara a rayuwarsa. Sai dai mene ne shi? Kuma a ina za mu same shi? Wasu suna ganin farin ciki yana tattare da tara dukiya, sai dai shin mawadata sun yi nasara kuma suna cikin farin ciki? […]

August 26, 2023

Sirrin Samun Nasara. Kashi Na Daya:

GABATARWA Dukkan yabo ya tabbata ga ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga fiyayyen halitta annabi Muhammad tare da iyalan gidansa tsarkaka. Wata kila zai iya zuwa kwakwalen da yawa daga cikin mata cewa: Mene ne sirrin samun nasara? Kuma ta kaka za mu isa ga cimma burinnmu? Kuma ta ina za […]

August 21, 2023

Rike Hannu A Sallah Ina Ya Samo Asali?

  Wato ba shakka wannan magana ta riqe hannu a sallah lamarine mai tsohon tarihi sama da shekara dubu hudu (4,000) da suka wuce. Ya kasance nau’ine na salon bauta ko girmama wani da ake ganin martabarsa da matsayinsa ga masu bin addinin “Zoroastianism” ko kace “Mazdayasna”, wanda akafi sani da “Majusawa”. Shi wannan addinin […]

July 27, 2023

Ranar Ashura:Ranar Juyayi (1)

Haka dai Husaini (a.s) ya ci gaba da ganawa da Ubangijinsa a daidai wannan lokaci alhali kuwa sojojin abokan gaba sai dada gabatowa suke yi. Tun kafin haka dai, Husaini (a.s) ya shirya sansaninsa inda ya tona rami a bayansa da kuma sanya wuta cikin ramin don hana abokan gaba bullo musu ta baya da […]

July 27, 2023

Daren Ashura; Daren Bankwana

A hakikain gaskiya dai wannan bukata ta Husaini (a.s) na a bashi wannan dare ba wai don yin tunani kan matakin da zai dauka ba ne ko kuma ci gaba da darasin yadda yanayin yake ba ne, a’a ai tuni ya riga da ya wuce hakan, don kuwa komai dai ya riga da ya fito […]

You are here: Page 1