January 26, 2024

GIRMAN SALATIN ANNABI YA WUCE MISALI

An tambayi ɗaya daga cikin Arifai (Shaikh Bahajat (R)) cewa: A ckin yi wa Annabi da Iyalinsa salati ana samun; Gafarar manyan zunubai, ɗimbin alhairai da albarka, aminci da biyan buƙatu. Ana kuma samun kusanci zuwa ga Allah Maɗaukaki, da tsira daga wuta, azabar ƙabari da kuma fitintinun ranar Alƙiyama, ana samun rabauta da shiga Aljanna da samun yardar Allah. Duk dai a cikin salatin Annabi. Shin me ya sa duk wannan?

Sai ya ce: “Ku yi duban ƙwaƙƙwafi a cikin Alkur’ani mai girma; Ba za ku samu ba face wata Aya ƙwaya ɗaya, wacce a cikinta Allah Maɗaukakin Sarki yake kiran Muminai su zo su yi wani aiki tare da shi, kuma tare da ɗukacin Mala’ikunsa duk za a taru a wannan aikin. (Kamar yadda ya faɗi (T)) Aikin shi ne: «Lallai Allah da Mala’ikunsa suna yin Salati ga Annabi, ya ku waɗanda kuka yi imani ku (ku ma) ku yi salati a gare shi ku yi taslimi sallamawa (Ku miƙa wuya miƙawa)»
Allahumma Salli Ala Muhammadin Wa Ali Muhammad

SHARE:
Makala 0 Replies to “GIRMAN SALATIN ANNABI YA WUCE MISALI”