February 25, 2024

IMAM MAHADI (ATF) FITILA HASKEN ALLAH

Al-Baqir Ibrahim Saminaka

Bismillah Wa Billah Allahumma Salli Ala Muhammadin Wa Ali Muhammad Wa Ajjil Farajahum Ya Karim… A koyaushe a yayin zagowar 15 ga watan Sha’aban, muminai bayin Allah sukan shirya abubuwa mabanbanta don taya juna murna da ranar haihuwar Limamin zamaninsu (ATF), maceci kuma mai shiryar da su, don faranta masa da neman yardar Allah (T). Bisa wannan ne na dasa alƙalamina a yau:

Allah Maɗaukakin Sarki a cikin littafinsa mai tsarki yana cewa: “Shi ne ya sanya rana a matsayin (Mai bayar da) ɗimi da haske da kuma wata a matsayin (Mai bayar da) haske kuma ya ƙaddara shi a matsayai (Daki-daki), kuma (Ya yi hakan ne) don ku san adadi -Ku gane lissafin- shekaru da kwanaki…” {Suratu Yunus Aya ta 10}.

Haƙiƙa wannan (Ƙwayar) ranar da ta game duniya ba kawai haske da ɗimi take bayarwa kawai ba, a’a (Masana ma sun tabbatar) ta na tana taka babbar wajen girmamar tsirrai da ababe masu rai. Ke nan dai a san da ta ɓace to rayuwa ba za ta yiwu ba saboda irin yadda suke a sarƙafe… Haka shi ma wata kyakkyawan haskensa ɗin nan shi ne fitilar da ke haska mana duhun dare, ba iya nan aikinsa ya taƙaitu ba, yana samar da natsuwa ga mutanen da ke rayuwa a doron wannan duniya… {Duba Mukhtasarul Amsal, na Shaikh Nasir Makarim Shirazi}.

Bisa duba na tsanaki zuwa ga wannan, muna iya jiyo ƙamshin hikimar da ta sanya Imam Sadiƙ (A) ya ba da misali da rana, a lokacin da sahabinsa Sulaiman ya tambaye shi cewa: “Shin ta yaya ne mutane za su amfana da Hujja (Imami) da yake a ɓoye?” Imam (A) sai ya amsa masa “Kamar dai yadda suke amfana da (hasken) rana ne a yayinda girgije ya lulluɓe ta” {Ƙadatuna… 4/473}.

Gini a kan wannan amsa ta Imam Sadiƙ (A), muna iya cewa: Kamar dai yadda rana ke taka rawar gani a tafiyar rayuwarmu, muke amfana da ita muna gane lissafi da adadin kwanaki, muke samun haske daga gare ta muke gudanar da al’amuranmu. Hakan nan muke amfanuwa da Imamul Hujja (ATF). Shi ne fitilar da ke hanske rayuwarmu, shi ne alƙiblarmu, shi ne ke tsaye a kanmu da kare mu daga faɗawa halaka… Muna amfana da shi fiye ma da hakan.

To wannan shi ne Imamin zamaninmu wanda ya faku, Limami na 12 cikin Limaman shiriya da tsira. Fitilar Allah Hasken Allah, Hujjar Allah Halifan Allah a doron ƙasa. Ku mu tashi mu nemi sanin shi, mu kuma sanar da mutane wane ne shi, wanda muke dako tare da addu’ar bayyarsa, wanda muke fata da kwaɗayin shiga cikin rundunarsa yardaddun Allah. Ina taya ɗaukacin muminai murnar zagowar ranar haihuwarsa Allah ya gaggauta mana bayyanarsa!

SHARE:
Makala 0 Replies to “IMAM MAHADI (ATF) FITILA HASKEN ALLAH”