June 2, 2024

Dattiijon arziki Allah yajikan Imam Khumaini (ks)

A ranar 14 ga watan Khordad shekarar 1368 (4 ga watan Yunin shekarar 1989), majalisar kwararru (ta zaban jagora) ta gudanar da taronta, inda bayan da Ayatullah Khamene’i ya karanta wasiyyar marigayi Imam Khumaini da ya dauke sa’oi biyu da rabi, ‘yan majalisar suka fara gudanar da tattaunawa da shawara kan wanda zai gaji Imam don zama jagoran Juyin Juya Halin Musulunci. Bayan sa’oi na tattaunawa, dukkan ‘yan majalisar sun amince da zaban Ayatullah Sayyid Ali Khamene’i (wanda a lokacin shi ne shugaban kasa) a matsayin sabon jagora. Ayatullah Khamene’i dai ya kasance daga cikin daliban Imam Khumaini (r.a) na kurkusa kana kuma daga cikin fitattun mutanen da suka ba da gagarumar gudummawa a Juyin Juya Halin Musulunci kuma daga cikin wadanda suka taimaka nesa ba kusa ba wajen kaddamar da yunkurin 15 ga watan Khordad, wanda ya tsaya kafada-kafada da sauran mataimakan juyin da ba da gagarumar sadaukarwa duk tsawon yunkurin Imam Khumaini da kuma dukkanin abubuwan da suka faru daga baya.

Shekara da shekaru kasashen yammaci da ‘yan amshin shatansu na cikin gida sun kasance cikin dakon wannan rana ta rasuwar Imam bayan sun yanke kaunar samun nasara a kansa. Sai dai farkawar al’ummar Iran da kuma saurin da majalisar kwararrun ta yi wajen zaban mutumin da ya dace da wannan matsayi na jagoranci da kuma irin goyon bayan da mabiya Imam suka yi wa zaben ta sanya makiyan cikin damuwa da kawo karshen mummunan fatansu. Don kuwa ba ma wai kawai juyin Imam bai zo karshe ba ne (kamar yadda makiyan suka so), face ma dai juyin ya sake bude wani sabon shafi ne na ci gaba da watsuwa da kuma karfi. Shin tunani, alheri da gaskiya suna iya gushewa?

A rana da daren 5 ga watan Yuni shekarar 1989 miliyoyin al’umma birnin Tehran da sauran al’ummomin da suka shigo garin daga garuruwa da kauyuka sun taru a babban wajen salla (musalla) na Tehran don yin ban kwana ta karshe da mutumin da ya dawo da mutumcin da daukaka (wa al’umma) a duniyar da take cike da duhu da zalunci ta hanyar yunkuri da juyinsa kana kuma ya watsa yunkurin komawa ga Allah Madaukakin Sarki da daukakar dan’Adam a duk fadin duniya.

Dukkanin abubuwan da aka yi a wajen jana’izar da hannun al’umma aka yi shi, cikin kauna da shauki. An dora jikin Imam mai tsarki a wani waje da kowa zai iya ganinsa yana rufe da koren kyalle tsakiyan miliyoyin masu juyayi, dukkansu cikin bakin ciki da zubar da hawaye alhali suna magana da Imaminsu cikin harshen da ya sawwaka ga kowa. Dukkanin hanyoyi da lungunan zuwa wajen sallar cike suke da jama’an da suke sanye da bakaken kaya don nuna bakin cikinsu, gidaje da shaguna kuwa duk an sanya musu tutocin juyayi da nuna bakin ciki, karatun Alkur’ani kuwa daga ko ina, masallatai, ofisoshi, ma’aikatu da gidaje sai tashi yake yi. Da daddare kuwa ko ta ina sai kyandir kake gani an kunna su don nuna alamun hasken da Imam ya zo da shi, duk sun haskaka wajen sallar da kewaye, alhali iyalai sun kewaye su (kyandir) suna kallon haskensu don tuntuni da irin hasken da jagoransu abin kaunarsu ya zo musu da shi.

Taken “Ya Husain” da masu juyayin suke rerawa alhali suna dukan kirji da kawunansu ya mai da yanayin wajen tamkar yanayin Ranar Ashurar da Imam Husaini (a.s) ya yi shahada. Bisa la’akari da cewa al’umma ba za su sake jin sautin Imam Khumaini dake cike da yanayin tunasar da mutum Ubangiji a Husaniyyar Jamaran ba, hakan ya kasance abin tashin hankali ga al’umma. Haka dai mutane suka ci gaba da zama a gefen jikin Imam mai tsarki duk tsawon dare har garin Allah ya waye, inda da sassafiyar ranar 6 ga Yuni shekarar 1989 aka yi masa salla karkashin limancin Ayatullah al-Uzma Golfaygani.

Babu shakka irin yawan al’ummar da suka fito don tarbar Imam Khumaini a ranar 12 ga watan Bahman shekarar 1357 (1 Fabrairu shekarar 1979) da kuma sake maimaita hakan a ranar jana’izarsa, duk suna daga cikin abubuwan mamaki na tarihi. Kafafen watsa labaran duniya sun tabbatar da cewa adadin mutanen da suka fito don tarbar Imam lokacin da ya dawo gida sun kai miliyan shida, amma wadanda suka fito don jana’izarsa sun kai mutanen miliyan tara. Hakan kuwa duk da cewa cikin wadannan shekaru goma sha daya na jagorancin Imam Khumaini kasashen Turai sun yi dukkan abin da za su iya wajen nuna adawarsu ga Jamhuriyar Musulunci da suka hada da kallafa mata yakin shekaru takwas da dai sauran makirce-makirce da ya sanya al’ummar Iran cikin mawuyacin hali na kunci da takurawa da kuma rasa abubuwan kaunarsu masu yawan gaske wanda a bisa dabi’a hakan zai sanya su gaji da kuma watsi da wannan juyi nasu, to sai dai ina hakan bai faru ba daga dukkan bangarori. Don kuwa al’ummar da suka tarbiyyantu a makarantar Imam Khumaini sun tasirantu da kuma imani da kalaminsa na cewa: “A duniya, gwargwadon girma da darajar manufa, gwargwadon karfin jurewa wahala, cutarwa, sadaukarwa da rashi na duniya ne”.

Bayan da bisne jikin Imam mai tsarkin ya ci tura sakamakon yawan jama’a, gidan radiyo ya sanar da daga jana’izar har zuwa wani lokaci da za a sanar nan gaba don haka jama’a su koma gidajensu. Sai dai jami’ai sun riga da sun san cewa lokaci bayan lokaci jama’a za su ci gaba da zuwa wajen jana’izar ne, don haka dai aka daure aka gudanar da ita a yammacin wannan rana duk kuwa da irin wahalhalun da ake fuskanta. Wasu kafafen watsa labaran duniya ma sun nuna wani sashi na wannan jana’iza.

Ta haka rasuwar Imam Khumaini, kamar rayuwarsa, ta kasance matakin farko na sabuwar wayewa da gwagwarmaya da kuma tabbatar da tafarki da ambatonsa har abada, don kuwa gaskiya abar tabbata ce matukar duniya tana ci gaba da wanzuwa.

 

® Hauwa Suleiman

SHARE:
Makala 0 Replies to “Dattiijon arziki Allah yajikan Imam Khumaini (ks)”