March 25, 2024

IMAM HASAN MAI KARAMCIN AHLUL-BAITI (A)

 

– Al-Baqir Ibrahim Saminaka

A yammacin wannan yini na 15 ga watan Ramadana, don tunawa tare da taya juna murnar zagowar ranar haihuwar Imamul Hasan ɗan Manzon Allah (A)… Zai kyautu mu ɗan tsakuri wani abu daga gare shi (A) domin wata ƙila ko ma dace mu amfana…

 

Ya zo a ruwaya cewa: Imam Hasan (A) wata rana wata baiwarsa ta ba shi kyautar cinkon fure. Nan take ya ce ma “Na ƴanta ki saboda Allah” Da ta yi yunƙurin jin ba’asi sai ya ce da ita “Haka nan Allah Maɗaukakin Sarki ya koyar da mu” [Duba Littafin Ƙādātuna na Ayatullah Sayyid Muhammad Hadiy Al-Husaini: 3/460].

Ire-iren waɗannan da wasu hadisosi suna nan da yawa da ke hakaito mana irin kyautatawa na Imam Hasan (A) waɗan suke zama masadiƙ na shahararren laƙabin nan nasa mai girma «كريم أهل البيت» Wato MAI KARAMCIN CIKIN AHLUL-BAITI (A). A daidai wannan bigeri ne za mu ɗan tsahirta mu dangwala daga kwarararsa (A).

 

KARAMCI…

A haƙiƙani da ma zahari; Faɗi da yalwar Karamci ya zarce «Kyauta» kawa, a’a ya tattare duk wata matan ta kyautata ta kowace fuska. Ba da kyauta, kyautatawa, So/fatan alheri ga mutane, jin zafin rashin damar tallafawa mutane, godiya ga masu karanci, afuwa da yafiya duk nau’i ne na karamci.

 

SABODA HAKA: Don kwaikwayon wannan sifa ta Imam (A), zai kyautu kowannenmu ya zama mai karamci (Kyautatawa/mutuntawa) ga kansa, mu zama masu karamci ga iyalai, makusanta da yan’uwanmu, masu karamci ga jama’armu, masu karamci ga aiyyuka ko sana’o’imu, masu karamci ga al’ummar da muke rayuwa a tsakaninsu, masu karamci ga aƙidunmu da kuma addininmu, kuma masu karamci ga kawukanmu. Halin/ɗabi’ar karamci da nufin kyautatawa ga kowa da kuma komai. Mu yi karamci mu kyautata!

 

Amincin Allah a gare ka ya Aba Muhammad Hasan Al-Mujaba, Imami ma’asumi, masmumi mazlumi. Da ku ne Allah ke gwararar falala da baiwa a cikin karamcinsa ya iyalan karamci, gabanku muke magiya ku roƙa ya kwarara mana ya maɓuɓɓugar alherai. Da wannan nake taya al’ummar Ma’aiki (S) murna da zagayowar ranar haihuwar jika kuma ɗansa Al-Hasan (A), Allah ya ba mu ikon kamata wannan hali na karamci, Allah ya karɓi ibadunmu bakiɗaya ya gafarta zunubanmu ya sanya mu daga cikin bayinsa ƴantattu a watan Ramadana.

SHARE:
Makala 0 Replies to “IMAM HASAN MAI KARAMCIN AHLUL-BAITI (A)”