March 25, 2024

TARIHIN IMAM HASAN(AS); DAN IMAM ALI(AS) Babban jika a Wajen Manzo s.a.w.a

 

Nasabarsa ta bangaren mahaifinsa: shine Hasan(as) Dan Ali(as), Dan Abu Talib(as), Dan Abdul-Muttallib…

Nasabarsa ta bangaren mahaifiyarsa: Shine Imam Hasan(as) Dan Sayyidah Fatimah Az-Zahra(as) ‘yar Annabi Muhammad(saw) Dan Abdullah, Dan Abdul-Muttallib…

Al-kunyarsa: Abu Muhammad.

Lakubbansa: Al-Mujtaba, Sayyid Shabab Ahlul-Janna, At-takiyyi, Az-zakiyyi, As-sibd, Ad-dayyiba, As-sayyid, Al-waliyyi…

Tarihin haihuwarsa: 15 Ramadan, Shekara ta 3 bayan Hijira, (wannan shine mashhuri, a wata ruwayar an ce shekara ta 2 bayan Hijira). Wanda yayi daidai da 4 Maris, shekara ta 625 Miladiyya, (1 Disemba 624 M).

Inda aka haifeshi: Madina.

Tambarin hatiminsa: Al-izzatu lillahi wahdah.

Tsayin rayuwarsa: shekara 48.

Tsayin shekarun imamancinsa: shekara 10.

Lokacin da ya fara Imamanci: 21 ga watan Ramadan, shekara 40 H (31 January 661 M).

Imamin da ya gabaceshi: Babansa; Imam Ali(as).

Imamin da ya gajeshi: Kaninsa; Imam Husain(as).

Tsayin lokacin halifancinsa: wata 6 (661 – 661 M).

Sarakunan zamaninsa: Mu’awiya dan Abu Sufyan.

Yakokin da ya halarta: Da shi aka yi dukkan yakokin da aka yi wajan bude kasashen Afrika da kasashen Farisa tsakanin shekara ta 25 H, zuwa ta 30 H, ya kuma bada gudunmawa sosai a duk yakokin da babansa ya yi na Jamal, Siffain da Nahrawan.

‘Yan uwansa: Imam Hasan(as) yana da ‘yan uwa wadanda suka hada Uba da Uwa da kuma wadanda suka hada Uba kadai. Masana tarihi sun yi sabani kan yawan ‘ya’yan Imam Ali(as), amma suna tsakanin 25 ne zuwa 33 a ruwayoyin daban daban. Wasu masana tarihi na cewa, ‘ya’yansa: 36, 18 da cikinsu maza ne, 18 kuma mata.

Matansa da ‘ya’yansa: Akwai sabanin masa sosai akan yawan matan da ‘ya’yan Imam Hasan(as). Wasu masana tarihi (irinsu Zahbi) sun zargi Imam Hasan(as) da yawan auri-saki, sunce ya auri mata daya-bayan-daya har fiye da 9.

(ﺳﻴﺮ ﺃﻋﻼﻡ ﺍﻟﻨﺒﻼﺀ ﻁ ﺍﻟﺮﺳﺎﻟﺔ، ﺍﻟﺬﻫﺒﻲ، ﺍﻟﺠﺰﺀ: 3، ﺻﻔﺤﺔ : 279).

Ibn Saa’d (27–28) yace; matan Imam Hasan(as) 3 ne da Sa-daka (Ummu-walad) 3, ‘ya’yansa maza 15, mata 9.

Wannan sabani ya samo asali ne daga bakar siyasar Banu Umayya, kasantuwar bayan Ma’awiya yayi fashi da makamin khalifanci, abinda yafi bawa muhammanci shine bata sunan Imam Ali(as) da Ahlinsa(as). (Siratun-Nawawiyya 1/342).

Kadan daga cikin mata da ‘ya’yan Imam Hasan(as) da masana tarihi suka fi ambata; duk da cewa akwai sabani da rashin tabbacin inganci ruwayar tarihi akansu:

(a) Matansa:

1. Ummu Bashir ‘yar Mas’ud Al-khazrajiyya.

2. Khaulatu ‘yar Manzur Al-fazariyya.

3. Ummu Ishak ‘yar Dalha At-taimi, wacce bayan Shahadarsa ta auri kaninsa Imam Husain(as).

4. Ja’ada ‘yar Ash’as, wacce ta saka masa gubar da tayi sanadiyyar shahadarsa da umarnin Ma’awiya Dan Abu Sufyan…

(b) ‘Ya’ya: 1. Zaid. 2. Al-hasan (mai sunan babansa). 3. Amr 4. Al-kasim. 5. Abdullahi 6. Abdurrahman. 7. Husain (ta kwaran Imam Husain(as), 8. Dalhah 9. Ummul Hasan. 10. Ummul husaini 11. Fadimah ‘yar Ummu Ishak. 12. Ummu Abdullahi. 13. Fadimah (ta 2) 14. Ummu Salama. 15. Rukayya…

Zuriyar Imam Hasan(as) sun bada gudunmawa sosai a fannoni daban-daban a tarihi, kuma har yanzu akwai wadanda nasabarsu take karewa zuwa Imam Hasan(as).

Wadanda nasabarsu take da dangantaka da zuriyar Imam Hasan(as) ana kiransu Sadat (Sayyid) ko Ashraf (Sharifi). Tabataba’i, Mudarris, Hakim, Shajariyan da Gulistana; wani yaki ne na Sadat al-Hasani (Zuriyar Imam Hasan(as).

Tarihin shahadarsa: 7 Safar 49 H. A wata ruwayar an ce 28 Safar ko Rabi’il Auwal, 50 H.

Inda ya yi shahada: Madina.

Dalilin shahadarsa: Gubar da Mu’awuya ya ba shi ta hannun matarsa Ja’ada ‘yar Ash’as.

Inda aka binne shi: Makabartar Bakiyya, Madina.

(Biharul anwar, juz’i na 39 – 40).

Ranar 15 ga watan Ramadan, shekarar hijira ta 3, gidan Annabci ya sanar da haihuwar jikan farko, nan take sai Manzon Allah(saw) ya garzaya zuwa gidan Fatima(as) don taya murna da farin ciki, yana zuwa sai aka gabatar masa da abin haihuwa mai albarka, Manzo(saw) ya tarbe shi, ya dauke shi a hannunsa, ya sumbace shi, ya rungume shi a kirjinsa; sai kuma ya kira Sallah a kunnensa na dama, ya yi Ikama a na hagu da sautin gaskiya da ya zama farkon sautin da ya fara ratsa samuwarsa da jinsa. Sai Manzo(saw) ya kalli Ali(as) ya ce: “Wane suna ka sa ma dana?” sai Imam Ali(as) ya ce: “Ban kasance mai shiga gabanka ba”, sai Manzo(saw) ya ce: ” Kamar yadda ban kasance mai shiga gaban Ubangijina ba”. Ana cikin hakan, sai ga wahayi wanda ke sanar da Monzo(saw) cewa Allah sanyawa abin haihuwan suna Hasan(as).

Da kwanaki bakwai da haihuwa suka kewayo, sai Manzo(saw) ya sami rago ya yi masa akika (yankan suna) da shi, daga ciki ya ba ungozoman da ta karbi haihuwarsa cinya tare da dinari guda, wannan a matsayin godiya bisa kokarinta a madadin abin haihuwa da mahaifiyarsa mai tsarki. Sannan ya kama kan abin haihuwa ya aske, ya yi sadaka da nauyin gashin da azurfa wanda ya yayyafe shi da (wani nau’in turare da ake kira da) Khaluk; sannan ya sa aka yi masa kaciya.

Wannan abu dai da Manzon Allah(saw) ya yi a ranar sunan Hasan(as) ya zamanto Sunnah ga Musulmi da suke koyi da ita.

(Zaka’ir al-Ukbah na Dabari, shafi na 120. Taufik Abu Ilm, cikin Ahlul-bait , shafi na 264).

Matsaiyin Imam Hasan(as) a Qur’ani da ingantattun hadisai:

Imam Hasan(as) yana daya daga cikin Ahlul-bayt(as) da ayar tsarkakewa (Ayatut-Tat’hir) ta sauka don nuna girman matsayinsu. Yana cikin wadanda Annabi(saw) ya lullube a bargo a Hadisul-Kisa’. Yana cikin wadan da aka ambata a ayar Mubahala (Ali-Imran : 61) da lamirin wakilin suna. Ya cikin wadanda aka wajabta sonsu da ayar Kauna (Surar Shura, 42 : 23). Atakaice duk wata aya da ta yabi Ahlul-bayt(as), Imam Hasan(as) yana cikinta.

Ta bangaren hadisan Annabi(saw), za mu ambaci kadan daga cikin matsayin Imam Hasan(as); kamar haka:

1. Bukhari da Muslim sun ruwaito daga Barra’u ya ce: Na ji Manzon Allah(saw), a lokacin yana dauke da Hasan(as) dan Ali(as) a kafadarsa, yana cewa:

“Ya Allah! lallai ni ina son mai sonsa”.

2. Tirmizi ya ruwaito daga Ibn Abbas ya ce: Manzon Allah(saw) ya kasance yana dauke da Hasan(as) dan Ali(as), sai wani mutum ya ce: “Ka hau mafi alherin abin hawa yaro”, Sai Manzo(saw) ya ce: “Kuma shi mafi alherin mai hawa ba”.

3. An ruwaito daga Anas bin Malik ya ce: An tambayi Manzo(saw) cewa: “Wa ka fi so daga mutan gidanka?” Sai ya ce: “Hasan(as) da Husaini(as)”.

4. An ruwaito daga UMMUL-MUMININ A’isha ta ce: Manzon Allah(saw) ya kasance yana daukar Hasan(as) ya rungume shi yana cewa:

“Ya Allah wannan dana ne, kuma ina sonsa don haka ina son wanda ke sonsa”.

5. An ruwaito daga Jabir bin Abdullahi, ya ce: Manzon Allah(saw) ya fadi cewa:

“Duk wanda ke son ya ga shugaban samarin gidan Aljanna sai ya kalli Hasan(as) bin Ali(as)”.

6. Abu Hamid al-Gazzali ya fitar, a cikin Ihya’u ulumul-din, daga Manzo(saw) yana cewa Hasan(as): “Ka yi kama da ni a halitta da halayya”.

7. Manzo(saw) ya ce: ” Hasan(as) da Husaini(as) Imamai ne, sun yunkura (sun nemi hakkinsu) ko sun zauna”…

Imam Sadiq(as) yana cewa:

“Imam Hasan(as) bin Ali(as) ya kasance mafi bautan mutanen zamaninsa, kuma ya fi su gudun duniya da daraja”.

” Imam Hasan(as) bin Ali(as) ya tafi Hajji har sau 25 da kafa. Ya kuma raba dukiyarsa biyu ya ba Allah rabi”.

Imam Hasan(as) ya taba bi ta wajen wasu mutane matalauta, a lokacin suna tsintar guntattakin gurasa da aka ci aka rage kuma aka watsar a hanya, suna ci. Da suka gan shi sai suka yi masa tayin ya zauna ya ci tare da su. Sai kuwa ya amsa musu da cewa: ‘Hakika Allah ba Ya son masu girman kai’, bayan da ya gama da su sai ya gayyace si bakuntarsa, sai ya yalwata su da dukiya mai yawa, ya kuma ciyar da tufatar da su”.

Wata rana an taba ce masa: “Me ya sa ba mu taba ganin ka ki amsawa mabukacin da ya tambaye ka ba?” sai ya amsa da cewa:

“Hakika ni ma mai rokon Allah ne, kuma mai kwadayi gare Shi; don haka ina kunyar in zama mai roko alhali kuma ina hana mai roko. Kuma Shi (Allah) Ya sabar da ni da bayar da ni’imarSa gare ni, haka ni ma na sabar da Shi in bayar da ni’marSa (da Ya ba ni) ga mutane; to ina tsoron in na yanke al’adata Shi ma Ya yanke al’adarSa ”.

Haka nan Imam Hasan(as) ya taba sayen wani lambu daga wasu mutane Ansarawa da kudi dirhami dari hudu, sai labari ya zo masa cewa (wadanda suka sayar masa din) sun koma suna bukata daga mutane, sai ya koma musu da lambun ba tare da ya karbi kudinsa ba.

Wannan kadan ne daga daga siffofinsa(as), kuma wani bangare ne na matsayinsa. Dabi’unsa sun kasance mafi tasiri wajen misalta kyawawan dabi’un Musulunci.

© Sheikh Abdurrahman murtala

SHARE:
Makala 0 Replies to “TARIHIN IMAM HASAN(AS); DAN IMAM ALI(AS) Babban jika a Wajen Manzo s.a.w.a”