January 28, 2024

YAKIN KHANDAK

 

Irin wannan karfi da Musulunci ya yi ya sanya Yahudawa suka ji cewa karfin Manzon Allah (s.a.w.a) babban hadari ne gare su, don haka sai suka shiga yin makirce-makirce ga da’awar Musulunci da Annabinsa, inda suka shiga jan hankulan makiya Musulunci don samar da wata babbar rundunar taron dangi don farwa Madina da gamawa da Musulunci.

Sai suka tuntubi kabilun Kuraishawa da Gatfan, suka dace da su a kan kai wa Madina hari da tsige da’awar Musulunci, sai dai labarin haka ya isa kunnen Manzo (s.a.w.a), don haka sai ya shawarci Sahabbansa kan yadda za’a bullo wa lamarin. Sai Salman al-Farisi (RA), wanda ke cikin zababbun Sahabbansa, ya ba shi shawarar da su kewaye Madina da rami, sai Manzo ya karbi wannan shawara, ya shiga haka rami tare da sauran Musulmi.

A bangare guda kuma Kuraishawa sun yi tanaji da kuma tara mazajensu, masu taimaka musu da sauran mabiyansu, ta yadda adadin rundunarsu ya kai mayaka dubu goma, suka kama hanyar Madina.

Shi kuwa Manzo (s.a.w.a) sai ya shirya Sahabbansa don yaki, adadinsu ya kai mayaka dubu uku.

Harin makiya ya fara yayin da Amru bin Abd Wudd al-Amiri ya ketare ramin, ya shiga yin barazana ga Musulmi yana kira da cewa: “Ko akwai mai fito-na-fito da ni?” Sai Ali bin Abi Talib (a.s) ya mike ya ce: “Ni ne gare shi ya Manzon Allah”. Sai Manzo (s.a.w.a) ya ce: “zauna Amru ne fa”.

Sai Amru bin Abdu Wudd ya maimaita kiransa, ya shiga yi wa Musulmi izgili. Sai Ali (a.s) ya mike ya ce: “Bar ni da shi Manzon Allah”. Sai Annabi ya kara cewa: “zauna Amru ne”. Sai Ali (a.s) ya ce: “Ko da Amru ne kuwa”. Sai Manzo (s.a.w.a) ya yiwa Ali izini ya ba shi takobinsa Zul-fikari, ya sanya masa garkuwarsa ya kuma nada masa rawaninsa, sannan Manzo ya ce:

A nan yana da kyau a fahimci cewa wannan jaddadawa da Manzon Allah (s) ya ke na cewa “Zauna Amru ne fa, ba wai yana yi ne don yana kokwanto Imam Ali (a.s) zai gaza ba ne wajen kashe Amru, face dai yana yi ne don ya nuna wasu abubuwa: Na farko dai ya nuna matsayin Imam Ali (a.s) na jaruntaka, na biyu kuma kana mafi muhimmanci yana so ne ya gwada sahabbansa ya gani ko wani zai taso ya fuskanci Amru ko kuma suna tsoro saboda sanin irin jaruntakar da Amru din yake da ita. To hakan kuwa ya faru don kuwa babu guda daga cikin sahabbai da ya yi ko alamar motsi wajen mikewa da fuskantar Amru, face ma dai sai kowa ya noke, kamar ba su yi imani da cewa idan Amru ya kashe su wajen kare Musulunci da Manzon Allah (s) za su shiga aljanna ba.

“Ya Allah wannan dan’uwana ne kuma dan baffana. To kar Ka bar ni makadaici don Kai ne mafi alherin Mai gadarwa(1)“.

Sai Ali ya gabata da kwazon nan na shi da ya saba, sai ya kara da Amru karawa mai tsanani, daga karshe dai ya bar shi kwance matacce.

Sai Musulmi suka yi kabbara yayin da suka ga Amru kwance a kasa kuma Ali na dawowa da nasara, sai Manzo (s.a.w.a) ya tarbe shi da fadarsa cewa:

“Sarar da Ali ya yiwa Amru bin Abd Wudd tafi ayyukan al’ummata har ranar kiyama

Da dare ya yi sai iska mai tsananin sanyi ta tashi, ta shiga fasa tukwane tana kashe wuta kuma tana karairaye haimomi. Wannan ya sa tsoro ya kama dakarun mushirikai, don haka sai suka sa kai suka bar Madina. Da wannan Allah Ya kaddarawa Musulmi nasara a wannan yaki da aka yi shi a shekara ta biyar bayan hijira.

Bayan an sami nasara a kansu, sai Kuraishawa suka koma Makka suna a tsiraice da kunya da wulakanta, sai Manzon Allah (s.a.w.a) ya shiga ladabtar da Yahudawa maha’intan abokan zama a Madina, wadanda suka saba alkawarinsu tare da Manzon Allah (s.a.w.a), suka yi makirci tare da Kuraishawa da kungiyoyinsu. Sai Allah kuwa ya dora Annabi a kansu, da wannan fitinarsu ta kare.

SHARE:
Makala 0 Replies to “YAKIN KHANDAK”