AMBALIYAR RUWA A KANO TA LALATA FIYE DA GIDAJE 1,000
Daga Baba Abdulkadir Hukumar nan da ke bada agajin gaggawa ta jihar Kano wato SEMA, ta ce, kimanin mutane 26 ne suka mutu, kana gidaje fiye da dubu ɗaya suka lalace sakamakon ambaliyar ruwa a kananan hukumomin jihar 4 na Kano, Shugaban hukumar Alhaji Saleh Jili ne ya bayyana hakan ga manema labarai […]