July 28, 2021

JAWABIN JAGORA GA MAHALARTA “TARON KASA-DAKASA KAN ‘YAN TAKFIRIYYA

JAWABIN JAGORA GA MAHALARTA “TARON KASA-DAKASA KAN ‘YAN TAKFIRIYYA

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai.

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Shugabanmu kuma Annabinmu al-Mustafa al-Amin Muhammad tare da Alayensa tsarkaka Ma’asumai da sahabbansa zababbu da wadanda suka biyo su cikin kyautatawa har zuwa ranar Lahira.

Da farko ina wa baki masu girma, mahalarta wannan taro masu girma, malaman mazhabobi daban-daban na Musulunci wadanda suka halarci wannan taro, barka da zuwa. Haka nan kuma ina mika godiya ta dangane da yadda kuka halarci wannan taron da kuma irin gudummawa mai amfani da kuka bayar yayin wannan taro na kwanaki biyu. Haka nan kuma wajibi ne in mika godiya ta ga manyan malaman Kum, musamman mai girma Ayatullah Makarim Shirazi da mai girma Ayatullah Subhani wadanda suka kirkiro wannan tunani da kuma aiwatar da shi a aikace. Alhamdu lillahi sun share fagen wannan aikin; wajibi ne a ci gaba da hakan. A takaice ina da masaniya kan jawabai daban daban da aka yi a wadannan ranaku biyu; to ni ma zan dan fadi wasu abubuwa:

Da farko wannan taro ne na tattaunawa kan kungiyar Takfiriyya (masu kafirta musulmi) wadda wata kungiya ce mai cutarwa da kuma hatsarin gaske ga duniyar musulmi. Duk kuwa da cewa wannan kungiya ta takfiriyya ba wata sabuwar kungiya ba ce, tana da tsawon tarihi, to sai dai cikin ‘yan shekarun baya-bayan ne ta sake kunno kai sakamakon makirce-makircen ma’abota girman kai ko kuma bisa taimakon kudaden wasu gwamnatocin yankin nan ko kuma bisa tsare-tsare da kulle-kullen kungiyoyin leken asirin kasashen ‘yan mulkin mallaka – irin su Amurka da Ingila da gwamnatin Sahyoniyawa – sannan kuma ta sami karfi. Wannan taro da kuma wannan yunkuri na ku na tinkara da kuma fada da wannan yunkuri na takfiriyya ne; ba wai kawai da wannan kungiya da a yau ake kira da kungiyar Da’esh (ISIS) ba. Kungiyar da a yau ake kiranta da Da’esh (ISIS), wani reshe ne na wannan lalatacciyar bishiya ta ‘yan takfiriyya. Amma ba ita ce dukkanin lamarin ba. Fasadi da lalatar da wadannan mutane suke aikatawa, wannan halaka shuka da ‘ya’yan dabbobi (kamar yadda ya zo cikin aya ta 205 na Suratul Bakara), wannan zubar da jinin mutanen da ba su ci ba su sha ba, wani bangare ne na danyen aikin wannan kungiya ta takfiriyya a duniyar musulmi. Da irin wannan mahangar ya kamata a kalli wannan lamarin.

Ina bakin ciki ainun, yadda a duniyar musulmi – maimakon mu yi amfani da dukkanin karfinmu wajen fada da makirce-makircen gwamnatin sahyoniyawa da irin wannan abin da take yi wa birnin Kudus da Masallacin Al-Aksa – amma sai ya zamana a yau an tilasta mana shagaltuwa da matsalolin da ma’abota girman kai suka haifar wa duniyar musulmi; babu kuma yadda za mu yi. A hakikanin gaskiya, magana da kuma kokarin magance matsalar ‘yan takfiriyya, wani lamari ne da aka dora wa malaman duniyar musulmi da masananta. Makiya sun tilasta wa duniyar musulmi matsalolin da ya zama wajibi su yi fada da su. To amma batu na asali, shi ne fada da gwamnatin sahyoniyawa; batu na asali shi ne batun Kudus; batu na asali shi ne batun Alkiblar musulmi ta farko, wato Masallacin Al-Aksa. Wannan su ne batutuwa na asali na duniyar musulmi.

Akwai wani lamari wanda ba za a iya inkarinsa ba, shi ne kuwa cewa kungiyoyin tafkiriyya da gwamnatocin da suke goyon bayansu, suna gudanar da ayyukansu ne wajen biyan bukatu da manufofin ma’abota girman kai da kuma sahyoniyawa. Ayyukansu suna lamunce wa Amurka da gwamnatocin mulkin mallaka na kasashen Turai da gwamnatin ‘yan mamaya ta sahyoniyawa ‘yan mamaya, manufofinsu ne. Akwai shaidu da alamu da suke tabbatar da hakan. Kungiyoyin takfiriyya suna jingina kansu ga Musulunci amma a aikace suna hidima ne ga ‘yan mulkin mallaka da ma’abota girman kai masu cutar da duniyar musulmi. Akwai shaidu da suke a fili, wadanda ba za a iya rufe ido kansu ba. A nan zan ambato wasu daga cikin wadannan shaidun:

Na farko shi ne cewa ‘yan takfiriyya sun sami nasarar jirkita yunkurin farkawa ta Musulunci daga ingantaccen tafarkin da yake tafiya a kai. Shi dai wannan yunkuri na farkawa ta Musulunci, wani yunkuri ne na kyama da adawa da Amurka, da mulkin kama-karya da ‘yan amshin shatan Amurka a wannan yankin. Wani yunkuri ne da al’ummomin kasashen arewacin Afirka suka faro shi ne don fada da girman kai da kuma Amurka. To amma ‘yan takfiriyyan sun sauya wa wannan gagarumin yunkuri na fada da ma’abota girman kan da kuma Amurka da ‘yan mulkin kama-karya mahanga, da mai she shi wani yakin basasa tsakanin musulmi da zubar da jinin juna. Isra’ila ita ce babbar abokiyar fada da yakin wannan. To amma ‘yan takfiriya sun mayar da titunan Bagadaza da babban masallacin Siriya da Damaskus da titunan Pakistan da garuruwa daban-daban na Siriya sun zamanto su ne fagen dagan.

Ku dubi halin da kasar Libiya take ciki a halin yanzu; ku dubi yanayin kasar Siriya, kasar Iraki da kasar Pakistan, ku ga da wa musulmi suke fada? Kamata ya yi a ce sun yi amfani da wannan karfi na su wajen fada da haramtacciyar kasar Isra’ila, to amma ‘yan Takfiriyya sun sauya mahangar wannan gwagwarmayar da shigo da shi cikin gida, cikin kan tituna da garuruwanmu. Suna tayar da bam a cikin babban masallacin Damaskus, su kan tayar da bama-bamai a tarurrukan mutanen da ba su ci ba su sha ba a birnin Bagadaza, su na kashe daruruwan mutane a Pakistan, kamar yadda ku ke ganin abin da ke faruwa a kasar Libiya. Dukkanin wadannan abubuwa suna daga cikin ayyukan ta’addancin wadannan kungiyoyi da ba za a taba mancewa da su ba tsawon tarihi. Sauya tafarki da mahangar wannan yunkuri (da ‘yan takfiriyyan suka yi) wani aiki ne da zai amfani Amurka da Ingila da kungiyoyin leke asirin Amurka da Ingila da MOSSAD da makamantansu.

Wata alama da kuma shaida ta daban ita ce cewa wadanda suke goyon bayan kungiyoyin takfiriyyar, suna hada baki da gwamnatin sahyoniyawa wajen yakar musulmi. Ba sa daga tsinke kan haramtacciya kasar Isra’ila, amma suna cutar da al’ummar musulmi da kulla musu makirce-makirce ta hanyar fakewa da batutuwa daban-daban.

Wata shaidar kuma ta daban ita ce cewa wannan fitinar da kungiyoyin takfiriyya suka haifar a kasashen musulmi – a Iraki da Siriya da Libiya da Labanon da sauran kasashe na daban – ta yi sanadiyyar rusa tushen wadannan kasashen. Ku dubi irin kudade da karfi da kayan aikin da lokacin da ake bukata wajen sake gina hanyoyi, matatun mai, ma’adinai, filayen jiragen sama, garuruwa da gidajen da aka rusa su sakamakon wadannan yakukuwa na basasa, sakamakon irin wadannan zubar da jini da aka yi. Wadannan suna daga cikin cutarwar ‘yan kungiyar takfiriyya ga duniyar musulmi cikin ‘yan shekarun baya-bayan nan…

Zamu cigaba…

 

SHARE:
Tattaunawa 0 Replies to “JAWABIN JAGORA GA MAHALARTA “TARON KASA-DAKASA KAN ‘YAN TAKFIRIYYA”