Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, ya yi afuwa ga fursunoni 46 da ke zaman gidan yari daban-daban a fadin jihar.
Da yake jawabi ga manema labarai jim kadan bayan afuwar, kwamishinan shari’a na jihar Barista Junaidu Attahir ya ce gwamnan ya yi wa fursunonin afuwa bisa shawarar kwamitin da aka kafa. Attahir ya ce gwamnan yana da ikon yafewa duk wanda aka samu da laifi kamar yadda kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya ya tanada. […]
Gwamna Ganduje ya sallami Baba Impossible daga kan Kujerar Kwamishinan Addinai
Cikin wata Sanarwa da Kwamishinan yada LABARAI Kwamares Muhammad Garba ya rabawa manema Labarai, yace Gwamnatin ta samu Baba Impossible wajen yin gaban Kasa na rage ranakun aiki ga Ma’aikan Ma’aikatarsa ba tare da tuntubar Gwamnatin ba wato ya rage musu ranakun Laraba da Jumu’a. Sannan Kuma baya biyayya ga Gwamnatin sau da Kafa. […]
Tsohon shugaban Katholika na duniya, Fafaroma Benedict ya rasu. Ya rasu yana da shekaru 95 a duniya.
Sama da al’ummar Habasha 100,000 da suka kaura sun koma gida
Hukumar kula da masu kaura ta MDD (IOM) ta ce, sama da al’ummar Habasha 100,000 da suka kaura ne suka koma gida daga kasashen waje, cikin watanni 10 na farkon bana. Tsakanin watan Junairu zuwa Oktoba, hukumar IOM ta yi wa mutane sama da 100,000 masu komawa Habasha rejista, inda mafi yawansu da adadinsu ya […]
Iyaye Da Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya Ta Yi Watsi Da Karin Kudin Makaranta.
Iyaye sun fara kokawa da karin kudin makaranta da wasu jami’oin kasar nan suka yi wasu kuma ke shirin yi, ita kuwa kungiyar daliban jami’oin kasar ta ce bazata sabu ba. Kungiyar daliban ta ce batun karin kudin makaranta a wannan yanayi da ake ciki zai kasance wata babbar matsala ga daliban da kuma […]
Kotu ta tabbatar da Oyebanji a matsayin gwamnan Ekiti
Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan a Jihar Ekiti ta tabbatar da nasarar Biodun Oyebanji a zaben gwamnan da aka gudanar a watan Yunin 2022. An bayyana Oyebanji, tsohon sakataren gwamnatin jihar (SSG), a matsayin wanda ya yi nasara a zaben, bayan ya lashe kananan hukumomi 15 daga cikin 16 na jihar. Oyebanji na jam’iyyar […]
Mutane 4 sun mutu sakamakon fashewar wani abu a Kogi.
An samu fashewar wani abu da safiyar yau Alhamis a Okene, jihar Kogi, inda ake fargabar mutuwar a kalla mutane hudu, kamar yadda rahoton ƴan sanda ya bayyana. Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa ya bayar da rahoton cewa, fashewar ta faru ne da misalin karfe 9 na safe. Lamarin ya faru ne a kusa […]
Rahotanni daga Brazil na cewa, tsohon dan wasan kwallon kafa na kasar Pele ya Rasu.
Rahotanni daga Brazil na cewa, tsohon dan wasan kwallon kafa na kasar Pele, wanda ya taba lashe kofin kwallon kafan duniya har sau uku, ya rasu jiya Alhamis yana da shekaru 82 a duniya, a wani asibiti dake birnin Sao Paulo, bayan ya yi fama da sankarar hanji, kamar yadda likitocinsa suka bayyana a hukumance. […]
Majalisa Ta Bukaci CBN Ya Tsawaita Wa’adin Daina Karbar Tsohon Kudi.
Majalisar Dattawa ta bukaci Babban Bankin Najeriya (CBN) ya tsawaita wa’adin daina karbar tsofaffin takardun kudi zuwa ranar 30 ga watan Yunin 2023. A ranar 15 ga watan Disamba CBN ya fara fitar da sabbin takardun kudi na N200, N500 da kuma N1,000, bayan sanya 31 ga watan Janairun 2023 a matsayin ranar daina […]