Ahlul Baiti

Jaridar Isar da Sakon Jikokin Manzon Allah (S.A.W)

June 12, 2023

Masarautar Saudiyya ta daga takunkumin hana ‘yan Shi’a ziyarar makabartar Baqi’a

Kamfanin Dillancin Labaran Fars ya ce ƙasar Saudiyya ta sassauta haramcin hana musulmi mabiya tafarkin Ahlulbayt (Shi’a) ziyarara tare da karanta addu’oi a makabartar Baqi’a da ke birnin Madina daga ranar 21 ga watan Yuni zuwa 1 ga watan Yuli.
Rahoton yace an ƙyale maza wadanda mafi yawa daga ƙasar Jamhuriyar Musulunci ta Iran suke su ziyarci makabartar ta Baqi’a wanda ake ƙira Jannatul Baqi.
Cikin limaman Shi’a goma sha biyu, akwai hudu da ke kwance a makabartar ta Baqi’a wato Imam Hassan dan Sayyeda Fatima bintu Rasulullah, Imam Ali Zainul-Abidin (dan Imam Husain), Imam Muhammad Baqir (dan Imam Zainul-Abidin) da kuma Imam Ja’afar Assadiq.
Daga dokar ta Saudiyya ya bai wa maziyartan damar karanta addu’oin ziyara a makabartar.
Dokar ta ce mata masu ziyara za su gabatar da addu’oin ne daga bayan katangar da ta kewaye makabartar.
Tun bayan sulhu da dawo da huldar jakadanci tsakanin ƙasashen Saudiyya da Iran ake ta samun sauye-sauye daga masarautar Saudiyya akan wasu al’amura da suka shafi musulmi ‘yan Shi’a.
Hakan na faruwa ne duk da irin yanda ƙasar Isra’ila da Amurka ke nuna adawa da kyautatuwan alaƙa tsakanin Saudiyyar da Iran.
A ranar Juma’a ne aka jiyo masarautar ta Saudiyya tana gargadi wa Amurka cewa za ta maida martani bayan da Amurkan ta sha alwashin ladabtar da ita a bisa kudirinta na rage yawan man da take haƙowa.

SHARE:
Labaran Duniya One Reply to “Masarautar Saudiyya ta daga takunkumin hana ‘yan Shi’a ziyarar makabartar Baqi’a”
Ahlul Baiti
Ahlul Baiti

COMMENTS

One comment on “Masarautar Saudiyya ta daga takunkumin hana ‘yan Shi’a ziyarar makabartar Baqi’a

    Author’s gravatar

    Alhamdulillah masha, Allah gaba dai gaba dai jinin fatima zahra s. a

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *