Ahlul Baiti

Jaridar Isar da Sakon Jikokin Manzon Allah (S.A.W)

October 4, 2022

WARWARE SHUBUHAR ‘YAN FITINA DA AKE KIRA DA SUNA ‘YAN SHI’AR LANDAN GAME DA (FARHATUZ ZAHRA “AS”)

 

Yaumu farhatuz zahra (AS) ma’ana ranar farin cikin Sayyida Fatima zahra (AS), wanda shine ranar 9 ga watan Rabi’ul Auwal.

– Wasu daga ‘yan shi’a suna farin ciki da bukukuwa a wannan ranar, domin shine ranar farko na Imamancin Imam Muhammad Al-mahdi (Atfs) wato Imami na 12.

 

– A daidai wannan rana ne kuma wasu yan fitina (‘yan shi’ar landan) suke bukukuwa da sunan a ranar ne aka kashe kalifa na biyu, sahabi Umar ibn kaddab, wanda wasu ma daga cikin su suna cewa a ranar ana dauke alkalami (abin nufi duk abinda bawa yayi babu rubutu ko bibiya a ranar), kuma suna kafa hujja ne da cewa: Ai Sayyida Fatima zahra (AS) ita ta assasa wannan rana, domin yin murna da mutuwar Sahabi Umar.

 

– Da farko shi sahabi Umar ibn kaddab idan muka duba zamu ga ya rasu ne a 26 ga watan zulhijja, shekara ta 23 bayan hijira, ita kuma Sayyida Fatima (AS) ta rasu a 3 ga watan jumada sani shekara ta 11 bayan hijira.

Kenan ta hanyar duba tarihin rasuwan su biyun zamu iya gane cewa: ita Sayyida Fatima (AS) ta riga shi rasuwa, da shi ya riga ta rasuwa sai muce da kanshin gaskiya a maganar su, amma ita ta riga shi, ya rasu ne a zulhijja ba a Rabi’ul Auwal ba a gaba daya, idan zata assasa murna zatayi ne bayan rasuwan shi, sai ya zamto s lokacin bata raye, zamu iya duba:

– فصل الخطال للشيخ أبو الحسين الخزئيني.

– عيد التاسع من ربيع الأول للشيخ محمد حسين الرجائي.

– فرحة الزهراء للشيخ حيدر الجبوري.

– القوب البديع في دفع الإشكالات عن عيد التاسع من ربيع الأول.

Zaka samu duka wancan ta’arifin suka kawo, ba na murna da kashe wani ba.

 

– Sannan maganar dauke alkalami a wannan rana bata da wani tushe ko makama domin hadisan da aka kawo ba mu’utabira bane ta janibin isnadi da sabawan da sukayi wa sunnah, duba littafin

مستدرك المسائل ج ٢، ص ٥٢٢

Domin karin bayani.

 

– Shi Sheikh Hussain Āli kashiful gida a littafin sa mai suna جنة المأوى  Juz’ na 1 shafi na 74 ya tafi akan cewa: “Sayyida Fatima (AS) tana murna a ranakun 9 da goman watan Rabi’ul Auwal ne saboda a wannan ranaku ne Mahaifin ta Manzon Allah (S) ya auri mahaifiyar ta Sayyida Kadija (AS) haka ta kasance tana raya wannan ranaku da farin ciki, bayan shahadan ta mabiyanta suka ci gaba da raya wannan ranaku, bayan shekaru masu yawa sai sunan فرحة الزهراء  din ya zama shi ya rage ma mabiyan nata, amma basu san abinda ya faru ba.

 

– Wasu Malaman na shi’a da sunnah suma sun tafi akan cewa: Ranar 9 ga watan Rabi’ul Auwal rana ne da aka kashe Umar Ibn Sa’ad (Shugaban rundunar umayyawa wadan da suka kashe Imam Hussain da sahabban shi a karbala), ba umar dan kaddabi ba, shima domin karin bayani zaka iya duba wadan nan litattafai:

 

ریاض العلماء و حیاض الفضلاء، الجزء: 4 ، صفحة: 381.

العاملي، جعفر مرتضى، الصحيح من سيرة الإمام علي، الجزء : 14 صفحة : 204.

 

A lokuta dayawa wadan nan yan kwangila aikin su shine jefo shubuha ko shafa baqin fenti wa shi’anci tare da haddasa husufa fadace-fadace tsakanin Musulmi, dalili akan haka kuwa shine: ta wancan bayanai zaka gane cewa sun kirkiri wannan rana ne da wannan suna domin a samar da matsala tsakanin Musulmi, a yayin da dan sunni yaji cewa dan shi’a yana farin ciki da kashe wani da yake ganin girma, me kuke ga zai faru?

YaAllah ka ganar da su, idan ba masu ganewa bane kuma mun barka da su domin kaine mai karfin da babu kamar sa.

 

 

© Emran Darussalam

SHARE:
Shubuhohi Da Raddodin Su One Reply to “WARWARE SHUBUHAR ‘YAN FITINA DA AKE KIRA DA SUNA ‘YAN SHI’AR LANDAN GAME DA (FARHATUZ ZAHRA “AS”)”
Ahlul Baiti
Ahlul Baiti

COMMENTS

One comment on “WARWARE SHUBUHAR ‘YAN FITINA DA AKE KIRA DA SUNA ‘YAN SHI’AR LANDAN GAME DA (FARHATUZ ZAHRA “AS”)

    Author’s gravatar

    Alhamdulillah,kai madalla da jaridar Ahlil-baiti(A S)Naji dadi sosai da samuwar wannan ci gaba.Ya Allah ka kara wa malumammu ilmi,juriya,lfy da hazaka.Ka kara kare mana su bihaqqi.Imamul-hujja(A F).

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *