Kwararru a Afirka sun ce kiwon lafiyar jama’a na cikin hadari yayin da ake fama da matsalar sauyin yanayi
Raunin tsarin kiwon lafiyar jama’a ya yi muni yayin da ake fuskantar matsalolin gaggawa na sauyin yanayi kamar ambaliyar ruwa, gurbacewar yanayi, da saurin yaduwar kwayoyin cututtuka, a cewar masana a taron tattaunawa da aka gudanar ta kafar bidiyo a ranar Talata a Nairobi, babban birnin kasar Kenya. Brama Kone, jami’in fasaha mai kula da […]
Iran: Shugaba Raisi Yace Shirin Amurka Na Maida Duniya Karkashinta Ya Kasa Samun Nasara
A lokacinda yake jawabi a babban taron MDD karo na 78 shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi ya bayyana shirin shirin Amurka dorawa dukkan kasashen duniya ikonta ya gaza kaiwa ga nasara. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana cewa a halin yanzu wata sabon tsaron duniya na kan haduwa, […]
Yemen: Ansarullah Ta Yaba Da Yadda Tattaunawa Take Tafiya Tsakanin Yemen Da Saudiya A Riyad
Kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ta bayyana cewa ya zuwa jiya Talata tattaunawa don kawo karshen yaki a kasar Yeman yana tafiya kamar yadda ya dace a birnin Riyad na kasar Saudiya. Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto Ali Al-Qoom mamba a kwamitin harkokin siyasa na kungiyar yana fadar haka, ya […]
An Bude Babban Taron Zauren MDD, Karo Na 78 A New York
An bude taron Majalisar Dinkin Duniya, karo na 78 a birnin New York na Amurka. A jawabinsa na bude taron, babban sakataren MDD, Antonio Guterres, ya nuna damuwa game da sauyin yanayi dake addabar duniya, wanda ke Haifar da bala’I iri daban daban. Mista Guteress, ya jajanta game da bala’in ambaliyar ruwa na Derna, […]
Motoci biyu ne aka kame makare da tabar wiwi da alburusai da ake kokarin shigowa da su Najeriya daga Ghana
Rundunar ‘yan sanda a jihar Kebbi dake arewacin Najeriya ta sanar da kame wasu manyan motoci biyu makare da kunshin tabar wiwi da kuma alburusai da ake kokarin shigowa da su Najeriya daga kasashen Ghana da jamhuriyar Benin. A lokacin da yake gabatar da motocin ga ‘yan jaridu a hedkwatar ‘yan sanda dake birnin Kebbi, […]
Hizbullah A SHirye Take Ta Fuskanci Barazanar Isra’ial Da Amurka A Kudancin Asia
Wani babban jami’ii a kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ya bayyana cewa kungiyar zata yi amfani da makamanta don kalubalantar HKI da Amurka a yankin Kudancin Asia. ya fadi haka a wani taron makokin wafatan manzon All..(s) da kuma shahadar jikokinsu masu tsari Imam Hassan da Imam Aliyu bin Musa (a) a kudancin birnin Beirut […]
UAE: Ba A Cire Takunkumin Biza A Kan ‘Yan Najeriya Ba
Wasu majiyoyi na gwamnatin UAE sun tabbatar da cewa, har yanzu kasar ba ta janye takunkumin hana ‘yan Najeriya bizar shiga kasar ba. A cikin ‘yan kwanakin nan dai wasu rahotanni daga fadar shugaban Najerya sun ce a wata tattanawa da aka yi tsakanin Tinubu na Najeriya da Muhammad Bin Zayid na UAE, sun […]
MDD Ta Mayar Wa Da Amurka Martani Akan Yankin Tudun Golan Dake Karkashin Mamayar HKI
Bayan da jakadiyar Amurka a MDD ta bayyana cewa; gwamnatin Joe Biden tana aiki ne da furucin da gwamnatocin da su ka gabace ta su ka yi na cewa; Yankin tuddan Gulan yaka karkashin Ira’ila ne, MDD ta bakin mai Magana da yawun babban magatakardarta cewa; Tuddan Gulan mallakin Syria ne wanda aka mamaye. […]
Me ya sa yankin Taiwan ba shi da ikon shiga MDD”
A jiya Alhamis da yau Jumma’a, babbar jakadiyar kasar Sin dake birnin Lagos na kudancin tarayyar Nijeriya Yan Yuqing, ta wallafa wani sharhi ta manyan kafofin watsa labaran Nijeriya, ciki hada da jaridar “This Day Live”, da jaridar “Guardian”, da jaridar “Vanguard”, da jaridar “Independent ”, da kuma jaridar “Lagos City Reporters” da sauransu. Cikin sharhin […]
MDD ta kaddamar da neman tallafi ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Libya
A Jiya Alhamis ne masu aikin jin kai da abokan hulda na MDD suka kaddamar da neman tallafi na dalar Amurka 71.4 don biyan bukatun gaggawa na ’yan Libya da ke fama da bala’in ambaliyar ruwa. Kudaden za a tallafawa mutane 250,000 ne daga cikin mutane 884,000 da aka kiyasta za su kasance mabukata nan […]