November 21, 2022

Ziyarar girmamawa da yan uwa Muhammadawa Kahfawa suka kawo wa Maulana Sheikh Bashir Lawal Kano (h) jiya Asabar 19-11-2023, daidai da 24-04-1444.

 

Daga birnin Zazzau wanda Sheikh Imani ya jagoranci yan uwan.

Jim kadan bayan sun kaiwa Sheikh Dr. Abduljabbar Kabara (h), ziyara a gidan ibada da ke Kurmawa cikin birnin Kano.

Kamar yadda irin wannan ziyarar ta kuma faruwa yau Lahadi 20-11-2022 dai-dai da 25-04-1444.

Wanda dattawan Kahfi suka kawo wa Sheikh Bashir Lawal Kano (h) Karkashin jagorancin shugaban dattawan Sheikh malam Ibrahim Kulkul (h) da sauran yan tawagarsa.

Dan karfafa alaka da zumunci mai dorewa tsakanin masoya Manzon Allah (sawa) da Ahlinsa tsarkaka da nagartattun Sahabbai.

Da fatan duka sun koma gida lafiya, Allah ya bar zumunci ya gaggauta fitowar maulammu Sheikh Abduljabbar Sheikh Nasiru Kabara Kano (r.a).

Alfarmar Manzon Allah (sawa) da Ahlinsa tsarkaka.

©WIS.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Ziyarar girmamawa da yan uwa Muhammadawa Kahfawa suka kawo wa Maulana Sheikh Bashir Lawal Kano (h) jiya Asabar 19-11-2023, daidai da 24-04-1444.”