January 9, 2023
Zimbabwe Ta Zama Gwarzuwar Dogaro Da Kai Ta Fuskar Samar Da Abinci A Nahiyar Afirka

A cikin shekarar 2022 da ta shude, kasar ta Zimbabwe ta zama gwarzuwa ta fuskar noma a nahiyar Afirka, inda ta girbe alkamar da ta kai ton 375,000.
Yawan alkamar da kasar ta Zimbabwe ta noma ya dora ta akan turbar zama mai dogaro da kanta a fuskar abinci.
An sami karuwar yawan alkamar da aka noma a kasar da kaso 13% idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata ta 2021.
A bana kasar ba za ta shigo da wata alkama daga waje ba, kuma za ta adana kudaden da suka kai dalar Amurka miliyan 300 da ta saba kashewa a kowace shekara.