August 31, 2021

Zamfara: ‘Yan Sanda Sun Sake Kwato Mutane 8 

Muhammad Bakir Muhammad
Hukumar yan sanda ta jihar Zamfara tace ta kwato wasu mutane 8 daga sansanin masu garkuwa da mutane. Bayanai dai sun nuna cewa mutanen an sace su ne a yankin Bungudu tun a ranar 25 ga watan Agustan wannan shekarar.
Jami’in hulda da jama’a a hukumar yan sandan jihar ta zamfara Sufurtanda Muhammad Shehu shine ya bayana hakan a garin Gusau yau Talata.
Ga bayanin kamar haka “Hukumar yan sandan jihar Zamfara a kokarin ta ba kare rayukan al’umma da dukiyoyin su ta kwato mutum takwas da aka yi garkuwa da su a ranar 25 ga watan Agustan 2021 a Kagon Sabuwa dake karamar hukumar Bugundu ta jihar Zamfara”
“Mutanen dai an dauke su zuwa sansanin masu garkuwa da mutane na Kungurmi…”
“An binciki lafiyar su Kuma suna koshin lafiya, kana kuma an sada su da iyalan su lafiya” In ji Muhammad Shehu.
Ya kuma tabbatar da cewa hukumar ta yan sanda zata cigaba da hada hannu da sauran hukumomin tsaro don kwato wadanda aka yi garkuwa dasu daga sansanin na masu garkuwa da mutane.
SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Zamfara: ‘Yan Sanda Sun Sake Kwato Mutane 8 ”