September 14, 2021

ZAMFARA: Yan Bindiga Na Hijira Don Neman Mafaka

Daga Muhammad Bakir Muhammad

______________________________________________________________________________________________

 

Sakamakon matakan kawo karshen matsalar tsaro da gwamnatin jihar Zamfara tare da hadin gwiwar gwamnatin tarayya suka dauka a yan kwanakin nan, zaman yan bindiga a yankunan na Zamfara ya kuntata kana kuma ya hana su gudanar da aiyukan laifuka da suka saba gudanarwa kari kuma da yunwa da matsin taltalin arziki ya tilasta musu gudu don neman mafaka a wasu wuraren daban.

Don kuntata musu din, gwamnatin tarayyan ta dau matakan katse layukan waya inda gwamnatin jahar Zamfara kuma ta rufe wasu kasuwanni a yan kwanakin da suka gabata.

Biyo bayan wadannan matakai kuma Gwamnan jahar ta zamfara ya bayyana cewa babu wani sauran sulhu tsakanin sa da yan bindigan. kamar dai yadda ya bayyana cewa aiyukan sojoji a yankin ya sanya yan bindigan sun fara neman hanyoyin sulhu.

Gwamnan ya bayyana cewa bayanan sirri sun riske shi cewa yan bindigan sun tuba kuma suna neman yin sulhu da gwamnatin sa.
Ya kuma bayya cewa wasu yan bindigan na tserewa zuwa wasu jahohin na daban don kuntatawar sojoji a jahar Zamfara.

 

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa ta gano wasu sabbin wuraren da yan bindigan suka yi hijira bayan tarwatsa sansanonin su a Zamfara. Ta bayyana cewa wuraren sun hada da:
Kebbe a garin Sokoto
Lambar Tureta shima a garin Sokoto
Birnin-Gwari a Kaduna
Jaridar ta bayyana cewa wani sananne a cikin yan bindigan ne mai suna Rekeb ya sanar da su matserar yan bindigan, inda kuma ya bayyana musu cewa shi da sauran manya daga yan uwansa suna nan zaune a Zamfara har yanzu.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “ZAMFARA: Yan Bindiga Na Hijira Don Neman Mafaka”