September 2, 2021

Zamfara: Dalibai 5 sun tsere daga sansanin masu garkuwa da mutane

Daga Muhammad Bakir Muhammad
Cikin satin nan labarin da ya karade kafofin sadarwa shine sace dalibai da akayi a jahar zamfara wanda adadin su yakai 74 daga makarantar sakandiren gwamnati na Kaya, karamar hukumar Maradun dake jahar zamfara.
Yan bindigan dai sun shiga makarantar ne da safiyar Laraba kana kuma sukayi awun gaba da dalibai 74 tare da malami.
Kasantuwar akwai dalibai da adadinsu yakai 400 a lokacin da yan bindigan suka shiga makarantar, dayawa daga daliban sunyi gudun ceton rai.
 Kamar yadda BBC tayi hira da mahaifin wata dalibar da ta tsere daga sansanin ‘yan bindigan, mutumin ya shaidawa BBC cewa ‘yar sa ta dawo gida ne da misalin karfe 1 na dare. Ya shaida musu cewa ‘yar ta fadamasa cewa wadanda suka sace su din sun raba su kashi biyu, a yayin da ake kokarin raba su din ne ita da wasu dalibai guda hudu sukayi sa’ar tsere wa.
Ya kuma kara da cewa mutum biyu daga daliban da suka tsere din yanzu haka suna asibiti ana duba su.
SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Zamfara: Dalibai 5 sun tsere daga sansanin masu garkuwa da mutane”