Zamba: Kotu ta ɗaure babban mai binciken kuɗi na jihar Yobe shekaru 5 a gidan yari

Kotun ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Muhammad Lawu Lawan ta yanke hukuncin ne a ranar Litinin.
Kotun ta ce ta kama Alhaji Yahya da laifi guda daya da ake zargin sa akai wato almundahanar Naira miliyan goma sha tara da dubu ɗari tara.
Tun farko dai hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Nigeria (EFCC), shiyyar jihar Borno ita ce ta gurfanar dashi gaban kotun kan wannan zargi.
A cikin wata sanarwa da hukumar EFCC ta fitar ta ce an zargi Alhaji Yahya da fitar da kudi daga ofishin babban mai binciken kuɗi na ƙananan hukumomin jihar Yobe a shekarar 2015 don sayan mota a hukumar amma sai ya karkatar da wani ɓangare na kuɗaɗen zuwa aljihun sa.
Daga.Abdullahi Abdulhamid.