March 18, 2023

ZABEN KANO, INEC TA KASHE BAKIN TSANYA

-Ta Soma Saka Sakamako a Shafinta.

Yanzu dai wai wai shiru. INEC ta soma saka sakamakon zaben da aka yi na Gwamna, sabanin shaci fadi da kirkira da wasu ke ta yi domin amfanin Jam’iyyar su.

Zuwa karfe tara da rabi na daren nan, a cikin sakamako guda 11222 a fadin jihar Kano, an saka guda 3840, wanda ya ke wakiltar kashi 34.22% a cikin dari na sakamakon.

Wannan ya karyata yadda wata Jam’iyya ta kirkiri wani shafi na bogi har ta ke nuna cewa Dan takarar ta ke kan gaba.

Bayan duba shafin da na yi, na fahimci cewa karya ce tsatsagwaro da wata jam’iyya ke cewa dan takarar ta ke gaba. Hasalima a iya cewa ba a san maci tuwo ba, domin ko rabin sakamakon INEC bata saka ba.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “ZABEN KANO, INEC TA KASHE BAKIN TSANYA”