October 31, 2021

Zaben jihar Anambra: Jami’an tsaro sun hallaka wasu mambobin IPOB

Daga Umar Musty


A cigaba da gabatowar zaben gwamnoni a jihar Anambra, jami’an sojin Nijeriya sun hallaka wasu mambobin kungiyar “a ware” ta Biafra (IPOB), kana kuma jami’in su guda ya rasa ran sa.

A bisa rahotannin hukumar sojin Nijeriya, sun kashe mutanen ne a titin Nnoni da ke kudancin karamar hukumar Idemili na jihar Anambra.

Mai magana da yawun hukumar sojin kasa, Birgediya janar Onyema Nwachuku a wata sanarwa da ya fitar jiya Asabat a binin Abuja, ya bayyana cewa matakin da suka dauka ya biyo bayan farmakin da mutanen suka kai kan jami’an tsaron da ke gudanar da aikin bada tsaro a shatale-talen Ekwulobia da ke karamar hukumar Aguata na jihar Anambra.

A bisa rahoton jami’in, hakan ne ya sanya jami’an tsaro suka shiga atisayen kame bata gari da ke yankin, sun fara daga titunan Nnewi da Nnobi inda a hakan ne suka yi gaba-da-gaba da su inda suka yi musayar watan da ta haifar da kisan mutane 4 daga cikin bata-garin.

Ya kuma kara da cewa daga cikin ganima, sun samu makaman da suka hada da bindiga kirar AK47, GALIL, Mota kirar hailanda, sai dai kuma abin jimami shine rashin daya daga cikin jami’an su da suka yi.

A wata atisaye ta daban da jami’an suka yi, jami’in ya bayyana cewa sun farmaki mambobin kungiyar “a ware” (IPOB) a yankin Umunze dake karamar hukumar Orumba.

Ya kuma bayyana cewa aiyukan mambobin na IPOB a yan kwanakin nan na da alaka da zaben da ke kara gabatowa a jihar, inda suke ababen da zai haifar da tsoro a zukatan al’umma don lalata sakamakon zaben.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Zaben jihar Anambra: Jami’an tsaro sun hallaka wasu mambobin IPOB”