Zaben 2023: Masu shirya tuggun ƙwacen na’urar tantance masu zaɓe, ko sayen ƙuri’u, ba za su yi nasara ba ~ INEC
Da
ga Abdulrashid Abdullahi, Kano
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ja kunnen ‘yan siyasa masu shirin ɗaukar hayar ‘yan daba domin su yi ƙwacen na’urar tantance masu rajistar zaɓe (BVAS), cewa shirme kawai su ke yi, ba za su yi nasara ba.
INEC ta ce baya ga shirin yin ƙwacen na’urar BVAS, ana ƙulle-ƙullen ɗaukar matasan domin su hargitsa aikin BVAS.
INEC ta ce idan wani ɗan jagaliya ya fizgi BVAS a ranar zaɓe ya gudu, to ya yi aikin banza, domin nan take INEC za ta kulle shi daina aiki.
Wannan ƙwarin guiwar ya fito ne daga bakin Mataimakin Daraktan Yaɗa Labarai da Fasahar Sadarwar Zamani (ICT), Lawrence Bayode, wanda furta haka a wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan talbijin na Channels TV.
A yayin tattaunawar, Bayode ya nuna yadda za a riƙa loda sakamakon zaɓe kai-tsaye ta hanyar amfani da na’urar BVAS, har ya ke cewa ita wannan na’ura ta na ɗauke da lambar sirri wadda za ta hana na’urar yin aiki matuƙar an ƙwace ta daga hannun jami’an INEC.
“Idan ‘yan jagaliyar siyasa su ka saci ko su ka ƙwace BVAS, to mu na da wuri na musamman wanda nan take za a danna don a hana BVAS ɗin aikin da ɓarayin ke so su yi da shi.”
Ya ce idan ma a wata rumfar zaɓe su ka kai BVAS ɗin da za su fizga, to Baturen Zaɓen da ke wurin zai saurin ganewa, ya kai rahoto ga jami’an tsaro.
Ya ce a wannan zaɓen za a riƙa fitar da adadin yawan ƙuri’ar da aka tantance a wurin zaɓen, tare da sakamkon zaɓen a lokaci guda.