July 31, 2021

ZA’A RANTSAR DA ZABABBEN SHUGABAN KASAR IRAN RANAR ALHAMIS MAI ZUWA

Daga Muhammad Bakir Muhammad

Ana sa ran rantsar da zababben shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi a ranar Alhamis mai zuwa 5 ga wata Augusta 2021.

Bisa rahoton da IRNA ta fitar, a zaman da ‘yan majalisu sukayi ranar 29 ga watan Yuli 2021 a taron da ya gudana a zauren majalisar dokokin kasar ta Iran sun cimma matsaya da kuma sanya 5 ga watan Augusta ta zama ranar rantsar da zababben Shugaban, wanda hakan zai gudana da yammacin karfe 5 na ranar Alhamis.

Kafin nasararsa na wannan karon, Ayatullah Ra’isi ya tsaya takarar neman shugabancin kasar Iran a shekarar 2017 sai dai kuma ya sha kaye a hannun Shugaba Hassan Rouhani wanda ya lashe shugabancin kasar a wa’adi na biyu.

Hakan bai sa ya janye ba, Rai’si a karo na biyu ya sake tsayawa takakar neman shugabancin kasar, inda kuma yayi nasara.

Kafin ya lashe zaben 2021, Ra’isi ya rike mukamin shugaban sashen shari’a na kasar Iran inda yake rike da wannan mukami tun daga shekarar 2019, daga bisa aka kuma nada shi mataimaki a kwamitin mutane 88 da ke zaɓar wanda zai zama babban jagoran addini a kasar.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “ZA’A RANTSAR DA ZABABBEN SHUGABAN KASAR IRAN RANAR ALHAMIS MAI ZUWA”