September 29, 2021

Za’a Katse Layukan Waya A Kaduna

Daga Muhammad Bakir Muhammad


Gwamnan jahar Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya ce mazauna Kaduna su zauna cikin shiri don katse layukan wayoyi a jahar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin hirar sa da wasu tashoshin rediyo. Inda ya bayyana cewa jami’an tsaro na shirye-shiryen kaddamar da farmaki kan yan bindigan da suke neman mafaka a wasu sassan jahar.

Gwamnan ya bayyana cewa katse hanyoyin sadarwan da za’ayi ba zai shafi dukkan fadin jahar ba, sai dai zai shafi dukkan kananan hukumomin da suke makobtaka da jahohin Zamfara da Katsina wanda sojoji ke aiyukan dakile matsalar yan bindiga a jahohin.

Ya kuma kara da cewa jami’an tsaro sun shawarce su da su katse layukan wayoyi a wasu sassan jahar, sai dai yace har zuwa yanzu suna jiran jami’an da su sanar da su kananan hukumomin da za’a katse da kuma lokacin da za’a katse.

Ya kuma ce “Sai dai inaso jama’ar Kaduna su san cewa in har aka bamu umarni gobe (Laraba), toh a goben zamu katse.

Gwamnan yayi bayanin ne da harshen hausa ya bayyana cewa sakamakon katse layukan waya da akayi a jahohin Zamfara da Katsina hakan ya sanya wasu daga yan bindigan sun tsallako zuwa garuruwan ketare da ke jahar ta Kaduna kana kuma suke kiran waya don neman kudaden fansa daga hannayen yan uwan wadanda suka yi garkuwa da su.

Ya bayyana cewa ko shakka babu, masu garkuwa da mutanen sun dogaro ne da wayoyi domin tuntubar junan su wurin samun bayanai da kuma tuntubar yan uwan wadanda suka yi garkuwa da su domin karbar kudaden fansa daga hannayen su.

Gwamnan ya ce tun wuri a rubuta takardar neman izini ga gwamnatin tarayya kan katse layukan wayan kana kuma shugaba Buhari ya amince da bukatar sa.

Gwamnan ya ja hankalin jama’ar Kaduna kan bada hadin kai ga jami’ai don gudanar da ayyukan su, inda yace duk mutumin da yazo sayan burodi da yakai adadi guda 20 zuwa 100 to a sayar masa amma a kai rahoto ga jami’an tsaro, ko kuma duk mutumin da ya kawo chajin wayoyin da adadin su yakai 20 don a yi masa chaji to a karba ayi masa amma a kai rahoton sa.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Za’a Katse Layukan Waya A Kaduna”