August 12, 2021

Za’a Janye Dokar Hana Amfani Da “Twitter” A Najeriya

Daga Baba Abdulƙadir
Gwamnatin tarayya ta ce za ta janye dokar da ta sanya na hana amfani da manhajar Twitter nan ba da jimawa ba.
Ministan yaɗa labarai da bunƙasa al’adu Alhaji Lai Muhammad ne ya bayyana hakan a ganawarsa da manema labaran fadar shugaban ƙasa da ke Villa a birnin tarayya Abuja bayan kammala zaman majalisar zartaswa a yau Laraba.
Lai Muhammad ya ce, ana gab da cimma matsaya kan matakin ƙarshe na samun matsaya dangane da dakatarwar da Najeriya ta yi wa kamfanin.
Sannan ministan ya yaba wa al’ummar Nijeriya sakamakon hakurin da suka yi bisa dakatarwar.
SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Za’a Janye Dokar Hana Amfani Da “Twitter” A Najeriya”