December 12, 2022

Za a samu saukin karancin wutar lantarki a Zimbabwe a shekarar 2023

Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya bayyana cewa, a shekarar 2023 dake tafe, jama’ar kasar Zimbabwe za su samu ci gaba sosai a fannin samar da wutar lantarki a kasar, yayin da gwamnati za ta kawar da shingayen zuba jari game da samar da wutar lantarki a kasar.
Emmerson Mnangagwa ya bayyana a shafinsa da yake wallafawa mako-mako a jaridar gwamnati ta Sunday Mail cewa, gwamnati za ta dauki matakai na musamman don tabbatar da ganin Zimbabwe ta fito daga matsalar karancin wutar lantarki.
Kamfanin Sinohydro na kasar Sin yana kafa sabbin injunan samar da wutar lantarki guda biyu a Hwange, inda aka samu karin karfin megawatt 600 tsakanin watan Disamba zuwa farkon shekarar 2023.
Baya ga samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da makamashin ruwa a kasar, wadda ke ci gaba da fama da fari da sauye-sauyen yanayi, kasar Zimbabwe za ta karkata kan sauran hanyoyin samar da wutar lantarki, kamar hasken rana, iska da iskar methane. Nan gaba kuma, kasar za ta mayar da hankali ne kan yadda ake shigo da wutar lantarki daga kasashe makwabta irin su Mozambik, wadda har yanzu ke da damar fitar da wasu makamashinta.

©cri (Safiyah Ma)

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Za a samu saukin karancin wutar lantarki a Zimbabwe a shekarar 2023”