April 14, 2023

Yin Sallar Tahajjud A Gida Ya Fi Lada

Shugaban Majalisar Malamai na Jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, ya bayyana cewa yin Sallar Tahajjud a gida ya fi lada da alheri kuma ba dole ba ne a tsawaita karatu ko a sauke Al-Kur’ani a cikin sallar.

Malamin ya yi wannan bayanin ne a yayin da al’ummar Musulmi suka dukufa wajen yin ibada a dararen kwanaki 10 na karshen watan Ramadan da aka shiga yanzu.

Mutum ya yi Sallar Tahajjud a gida ya fi alheri, ya fi albarka ya fi lada,” in ji Sheikh Ibrahim Khalil, a wata hirar da ya yi da freedom radio,

A dararen kwanaki 10 na karshen watan Ramadan ne dai Musulmi suka fi dukufa wajen yin ibada, inda suke yin fitar dango maza da mata zuwa masallatai da tsakar dare domin yin Sallar Tahajjud da neman dacewa da Daren Daraja (Lailatul Kadari).

Akasari ana sauke Al-Kur’ani a kwanaki 1o da ake yin a sallar tahajjud inda ake karanta izu shida a kowane dare.

Irin wannan jajircewa na da nasaba da irin kwadaitarwar da malamai suka yi game da falalar sallar da falalar daren Lailatul Kadari; Uwa uba, koyi da Manzon Allah (SAW) wanda a dararen yakan ninninka yanayin yadda yake ibada tare da karfafar iyalansa su yi hakan.

A kan haka ne Sheikh Ibrahim Khalil, ya bayyana cewa idan mutum ya yi Sallar Tahajjud a gida ta fi lada kuma ya fi alheri.

 

 

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Yin Sallar Tahajjud A Gida Ya Fi Lada”