August 19, 2023

​Yemen: Wata Tawagar Sasantawa Daga Kasar Omman Ta Isa San’aa A Ranar Alhamis

 

Wata tawagar sasantawa tsakanin kasar Saudiya da kuam Yemen ta isa birnin San’aa babban birnin kasar Yemen a safiyar ranar Alhamis don ci gaba da tattaunawa dangane da kawo karshen yaki a kasar, sannan batun jinkai na daga cikin ajendar haduwar bangarorin biyu.

Tashar talabijin ta Almayadeen da kasar Lebanon ta nakalto shugaban tawagar mashawarta ta gwamnatin kasar Yemen Muhammad Abdussalam yana fadar haka. Kafin haka dai shugaban kungiyar Ansarallah Sayid Badrudden Huthi ya bayyana cewa halin da kasarsa take ciki na ci gaba da killace kasar ta sama da kasa da kuma mummunan halin da mutanen kasar suke ciki sanadiyyar haka ba zai ci gaba ba.

Tun watan Afrilun da ya gabata ne tawagar kasar ta Saudiyya ta shiga tattaunawa kai tsaye da jami’an gwamnatin san’a, inda bangarorin biyu suka tattauna al-amura wadanda suka hada da na jinkai fursinonin yaki da kuma tsagaita budewa juna wuta na din din din.

Jami’an gwamnatin kasar Yemen sai suna tuhumar kasar Saudiya da jan kafa wajen tattaunawa da kuma kawo karshen yakin saboda shihsigin da Amurka da burtaniya suke yi a cikin al-amuran kasar ta Saudiya.

 

 

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Yemen: Wata Tawagar Sasantawa Daga Kasar Omman Ta Isa San’aa A Ranar Alhamis”