November 10, 2023
Yemen ta ƙware wajen yaƙi: “Tun bayan da kasar Yemen ta sanar da shiga cikin yaki a hukumance tare da gwagwarmayar Palastinawa a Gaza, kusan kowace rana suna ci gaba da kai hare-hare, har zuwa kwanan nan jami’an tsaron haramtacciyar kasar Isra’ila sun yi ta kokarin boye barnar da aka yi musu amma a hankali yana bayyana. da kafofin watsa labarai na Yamma suma basa fada. Wadannan hare-haren da sun faruwa ba sau daya ba ba biyu ba, Amma isowar jirage marasa matukai na Yemen da makamai masu linzami shi yafi tayar musu hankali da hatsari, saboda yana da alaƙa da yiwuwar hakan ya shafi wasu wurare masu yawa, kamar “Bab al-Mandab” da garuruwan dake kusa da Bahar Maliya.
