September 20, 2023

​Yemen: Ansarullah Ta Yaba Da Yadda Tattaunawa Take Tafiya Tsakanin Yemen Da Saudiya A Riyad

 

Kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ta bayyana cewa ya zuwa jiya Talata tattaunawa don kawo karshen yaki a kasar Yeman yana tafiya kamar yadda ya dace a birnin Riyad na kasar Saudiya.

Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto Ali Al-Qoom mamba a kwamitin harkokin siyasa na kungiyar yana fadar haka, ya kuma kara da cewa da farko an sanya batun jinkai a matsayin matsala ta farko wacce yakamata a fara warwareta.

Ya kuma kammala da cewa tare da shiga tsakani na kasar Umma tattaunawa tsakanin bangarorin biyu a cikin kwanaki 5 da aka dauka aka tattaunawa muna fatan za’a haifar da da mai ido.

Tun shekara ta 2015 ne gwamnatin kasar Saudia da kawayenta na kasashen Larabawa da wasu kasashen yamma suka fadawa kasar Yemen da yaki da sunan maida tsohon shugaban kasar Abdu Rabbu Mansur Hadi kan kujerar shugabancin kasar. Manufarda basu cimma ba har zuwa yanzu.

 

©voh

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Yemen: Ansarullah Ta Yaba Da Yadda Tattaunawa Take Tafiya Tsakanin Yemen Da Saudiya A Riyad”