April 16, 2023
Yemen: An Fara Musayar Fursunonin Yaki Tsakanin Gwamnatin San’a Da Saudiyya

A yau Asabar ne jirgin da ke dauke da fursunonin Houthi ya tashi daga kasar Saudiyya, inda zai nufi birnin Sana’a, inda daga nan ne masarautar Saudiyya za ta karbi wani jirgin da ke dauke da fursunonin Saudiyya, a rana ta biyu na wani gagarumin aikin musayar fursunoni.
“Jirgin farko ya taso ne daga Abha (kudancin Saudiyya) zuwa Sana’a, tare da tsaffin fursunoni 120,” in ji Jessica Mosan, mai baiwa kungiyar agaji ta Red Cross shawara kan harkokin yada labarai.
Tun da farko gwamnatin Yemen ta sanar da kammala musayar fursunoni da kungiyar Houthi ta Ansar Allah, da kuma isowar jiragen sama guda biyu dauke da fursunoni daga bangarorin biyu zuwa filayen saukar jiragen sama na Aden da Sana’a a lokaci guda.
Kwamitin hadin gwiwar kasashen yankin Gulf na maraba da fara shirin musayar fursunoni, kuma sun dauki yarjejeniyar a matsayin wani haske na fatan dora rikicin kasar Yemen kan hanyar samun mafita.