August 19, 2023

Yawan masu fama da yunwa a Arewa maso Gabas na tayar da hankali’

  1. Najeriya ta ce akwai mutum miliyan 4.3 da ke fama da yunwa a jihohin Borno da Adamawa da kuma Yobe, lamarin da ya zama abin tashin hankali ga ayyukan jin ƙan ɗan’adam.

Babban jami’in tsara ayyukan jin ƙai a Najeriya, Matthias Shemale ne ya bayyana haka ranar Juma’a yayin wani tattaki da jami’an ayyukan jin ƙai suka gudanar a Abuja a wani ɓangare na Ranar Jin Ƙai ta Duniya.

Ya buƙaci a sake nazari a kan yiwuwar amfani da ƙarfin soja kan Nijar, don kuwa a cewarsa, shiga yaƙi zai ta’azzara buƙatun agaji da ake da su ba kawai a Nijar ba, har ma a ita kanta Najeriya saboda iyakar da suka haɗa.

Ma’aikatan agajin sun ce tattakin wata azama ce don nuna jajircewa kan ayyukan agaji da jin ƙai a yankunan da ke fama da rikice-rikice da kuma ambaliyar ruwa.

Daga 2016, an kashe masu aikin agaji 37 a jihohin Borno da Adamawa da kuma Yobe, tare da raunata 24, baya ga yin garkuwa da 34.

©Bbc hausa

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Yawan masu fama da yunwa a Arewa maso Gabas na tayar da hankali’”