YAU JUMA,A RANAR QUDUS TA DUNIYA.

RANAR QUDUS TA DUNIYA TA NA SA AL’UMMAR PALASTINU SU FAHIMCI CEWA; AKWAI WADANSU MUTANE A BANGARORI DABAN-DABAN NA DUNIYA DA SU KE DAMU DA HALIN DA SUKE CIKI:
Ranar Jumu’a ta karshe ta ko wane watan Ramadan; rana ce da marigayi Imam Khomeini(qs) ya ware a matsayin Ranar Qudus ta duniya; tun a shekara ta 1979 (shekarar farko bayan cin nasarar juyin musulunci a Iran).
Don haka, a ranar Qudus, dukkanin al’ummar musulmi ke fitowa; kwan su da kwarkwatar su, don nuna goyon baya ga Palasdinawa da ake zalunta da kuma yin tir da Allah waddai da ta’addancin Yahudawan Sahayoniya.
Imam Khomeini(qs) ya kasance mai neman hakkin alummar Palasdinu da kyamar mamayan Yahudawan Sahayoniya ga Palasdinu tun shekaru masu yawa kafin cin nasarar juyin musulunci a Iran. Bayan da aka sami nasar juyin Musulunci, farkon aikin da Imam(qs) ya fara yi game da wannan dadadden tunani na sa, Shine rufe ofishin jakadancin haramtacciyar kasar Israila da kuma mika ofishin nasu ga masu gwagwarmayar ‘yantar da Palasdinu.
JAWABIN IMAM KHOMEINI(QS) AKAN RANAR QUDUS:
“…. Ina gayyatar dukkan Musulmin duniya da suware juma’ar karshe ta watan Ramadan mai tsarki a matsayin ranar Qudus. Lokacin da za su shelanta goyon bayan Musulmi ga hakkokin Musulmin Palasdinu da aka danne.
A tsawon shekaru da dama na sha fadakar da al’ummar Musulmi a kan irin hadarin da kasar mamaya ta Isra’ila ta ke da shi. Wacce a yau ta tsananta hare-haren da ta ke kaiwa yan’uwanmu Palasdinawa maza da mata. Wanda musamman a kudancin Labanon ta ke kai harin bama-bamai kan gidajen Palasdinawa da nufin murkushe gwagwarmayar Palasdin.
Ina mai kira ga dukkanin
Musulmi a duniya, da gwamnatocin kasashen Musulmi, su hada hannu su katse hannun wannan kasa mai mamaya da magoya bayanta.
Ina kira ga Musulmi a duk duniya, da su maida ranar Juma’ar karshe na Ramadana mai tsarki ranar Qudus. Wanda shi kansa wani lokaci ne na fayyacewa, wanda a gaba zai iya zama mai fayyace makomar Palasdin. Wanda a wani biki za a nuna goyon bayan Musulmi na duniya ga hakkokin wadannan mutane Musulmi.
Ina mai rokon Allah da ya baiwa Musulmi nasara a kan Kafirai.”
—- Imam Khomeini(qs) (August, 1979).
Ranar Qudus dai ba ta ta’allaka ne da kasar Iran ko Musulmi kawai ba; rana ce ta duniya. Kiran Imam Khomeini(qs) da nuna goyon baya ga gwagwarmayar Palasdinawa a ranar Jumu’ar karshe na watan Ramadan sai kara karbuwa yake yi a tsakanin alummar musulmi da sauran alummu masu son ‘yanci a fadin duniya baki daya, duk fadin duniya, al’ummar musulmi da sauran al’ummu masu bige da neman ‘yanci, suke bayyanar da kasantuwarsu a fili don nuna goyon baya da kuma ba da kariyarsu ga ‘yan’uwansu Palastinawa. A wannan ranar, al’ummu suna tabbatar da iradar da suke da ita ce wajen fuskantar albarusan haramtacciyar kasar Isra’ila a kasar Palastinu da ake zalunta.
Zagayowar Ranar Qudus ta Duniya, tana sake jaddadawa da kuma tunatar da musulmin duniya (masu kishi) ne nauyin da yake (wuyansu) wajen ba da kariya da kuma goyon bayan al’ummar Palastinu da ake zalunta.
Wadannan mutane da suke cikin yankunan (Palastin) da aka mamaye sannan kuma cikin rauni da hali na zalunta (da suke fuskanta) suke gwagwarmaya sannan kuma suke fuskantar wahalhalu – wanda babban fatan kawai da ake da ita wajen ‘yantar da Palastinu da kawar da gwamnatin zalunci da ‘yan fashi (ta yahudawan sahyoniya) ta ta’allaka ne da wannan gwagwarmaya ta cikin gida – wajibi ne su ji sannan kuma su san cewa a dukkanin fadin duniyar musulmi, zukatan al’ummomi cike suke da tunanin (irin halin da suke ciki) kuma za su ci gaba da goyon baya da ba su kariya.
Matukar dai muna son wadannan ‘yan gwagwarmaya wadanda suke tamkar baki a cikin gidajensu su ji cewa (lalle muna tare da su), to wajibi ne mu gudanar da irin wadannan zanga-zangogi da jerin gwano na al’umma a dukkanin fadin duniyar musulmi.
Ta hanyar ranar Qudus ta duniya Al’ummar Palastinu da ake zalunta za su fahimci cewa akwai wadansu mutane a bangarori daban-daban na duniya da suka damu da halin da suke ciki.
© Abdulrahman Murtala.