January 7, 2023

YAU A KE BIKIN KIRSIMETI A KASAR HABASHA (ETHIOPIA 🇪🇹) DA SAURAN WASU KASASHEN DUNIYA DA KE BIN DARIKAR ORTHODOX 7/1/2023

C IIikin Shagulgular gudanar da Bukukuwan ibada na Kirsimeti a Habasha, Da Akwai Bikin Ganna.

Ganna biki ne na addini na masu ra’ayin Yan Mazan jiya, tare da Al’adunsu na musamman. Bayar da kyaututtuka ba shine mafi girman Al’ada a Kirsimeti a Habasha ba, a’a, su fi mai da hankali kan al’ada da bikin.

Yawancin Habashawa suna yin azumin kwanaki 43 kafin ranar Kirsimeti.

Ana fara azumi ne a ranar 25 ga Nuwamba, Ranar da aka fi sani da Tsome Nebiyat (Azumin Annabawa), kuma ana gudanar da shi har zuwa 7 ga Janairu.

Yan Habasha suna cin abinci sau ɗaya a rana tsawon kwanaki 43, abincin ya kamata ya kasance ba tare da nama, Nono Da
Madara, da kwa,i waɗanda duk lokacin azumi za’a Amfani Dasu.
(Mai Azumi Ba zaici Ba)

Mazauna yankin su na yin ado da fararen kaya a ranar Kirsimeti.

Mutane da yawa suna sanya kayan Gargajiya da ake kira Netela.

Kirsimeti a Habasha ana kiransa da suna “Ganna ko Genna” kuma ana yin bikin ne a ranar Bakwai ga watan Janairu.

Kamar yawancin majami’un Orthodox na duniya, bikin Kirsimeti ya na gudana ne a ranar 7 ga Janairu a Habasha (Ethipia).

Kamar dai yadda watannin kalandar Habasha suka bambanta, bikin Ganna ya kasance ne a ranar 29 ga watan Tahsas.

Cocin Orthodox na Habasha ta ɗauki 7 ga Janairu a matsayin ranar haihuwar Yesu don haka ita ce ranar manyan ayyukan addini a Habasha.

A Wata tatsuniyar Habasha ta yi iƙirarin cewa makiyaya sunji labarin haihuwar Yesu, nan ta ke su ka soma biki. sun soma Bikinne ne da wasa ba tare da bata lokaci ba ta amfani da sandunansu na katako mai kama da hockey.

Saboda haka, a Ranar Kirsimeti galibi yara maza da samari suna yin wasa irin na wasan hockey da sandar katako mai lankwasa da ball.

Ana kiran wasan Yágenna Chewata, ko kuma genna a takaice.

Shekarar da muke ciki a Habasha ita ce shekarar 2015. Shekarar Habasha za ta farawa ne a ranar Ranar Talata 12 Ga Satumba ko kuma a ranar 13 ga Satumba a shekara ta miladiyya.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “YAU A KE BIKIN KIRSIMETI A KASAR HABASHA (ETHIOPIA 🇪🇹) DA SAURAN WASU KASASHEN DUNIYA DA KE BIN DARIKAR ORTHODOX 7/1/2023”