May 29, 2023

Yanzu-Yanzu: Tinubu ya zama rantsastsen Shugaban Najeriya

 Alkalin Alkalan Najeriya Ariwoola ya rantsar da Tinubu sabon shugaban kasan Najeriya da misalin karfe 10:37 dai dai

 

An rantsar da Bola Ahmed Tinubu a matsayin sabon shugaban Najeriya kuma kwamandan dakarun sojin Kasa.

 

Alkalin Alkalan Najeeiya Kayode Ariwoola shine ya jagoranci rantsar da sabon shugaban kasan a safiyar yau Litinin da misalin karfe 10:37 dai dai.

 

Shugaban Kasa Ahmed Tinubu ya hau mimbari tare da mutane kamar haka; Mai dakin sa Sanata Oluremi Tinubu tare da kuma Mai dakin tsohon shugaban kasa Malama Aisha Buhari.

 

Kafin rantsar da Ahmed Tinubu, an fara da rantsar da mataimakin sa Kashim Shettima da kisalin karfe 10:28 na safiyar yau!

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Yanzu-Yanzu: Tinubu ya zama rantsastsen Shugaban Najeriya”