September 24, 2021

Yanayin Zamantakewa Da Siyasa Bayan Karbala


Bayan faruwan kisan gillan Ashura a duk fadin duniyar musulmi inda labarin hakan ya isa wajen, musamman a Hijaz da Iraqi, Yan Shi’a da magoya bayan imamai (AS) sun shiga cikin wani irin yanayi na tsoro da fargaba. Don kuwa ana jin cewa gwamnatin Yazid ta shirya tabbatar da ikon ta ta kowacce hanya, ciki kuwa har da kisan imam Hussain (AS) wanda ‘Dan manzon Allah (SAWA) ne, wanda kuma yake da matsayi da daukaka a dukkanin duniyar musulmi. irin wannan tsoro da fargaba wanda ake iya ganin alamar sa a Kufa da Madina, ya karu. wanda daya daga cikin su shine murkushe yunkirin Al-harrah da kuma irin dirar mikiya mai tsanin gaske da ake yi wa yankunan da Ahlulbaiti suke da tasiri, wato Hijaz musamman Madina, haka nan Iraqi musamman Kufa. Alaka ta yi rauni sannan magoya bayan Imamai kuma masu adawa da hukumar banu umayya sun kasance cikin rauni da shakku.

An nakalto wata ruwaya daga Imam Sadiq (AS) cewa a lokacin da yake magana kan yanayin Imaman da suka gabace shi, yana cewa “mutane sun yi ridda bayan Husain in banda mutane uku” wato bayan Imam Husain (AS) mutane sunyi ridda in banda mutane uku, a wata ruwayar in banda mutane 8, a wata ruwayar in banda mutane 7. A wata ruwayar kuma da aka ruwaito daga Imam Sajjad (AS) wanda Abu Umar Mahdi ne ya ruwairo ta yana fadin cewa ” Na ji imam Sajjad yana fadin cewa babu mutane 20 a Makka da Madina da suke son mu”, wato a duk fadin garuruwan Makka da Madina babu mutane 20 da suke son mu.

Na kawo wadannan hadisai guda 2 ne don mu fahimci irin yanayi na gaba daya da duniyar musulmi ta shiga. Wato irin wannan yanayi da tursasawa da amfani da karfi suka haifar ta yadda magoya bayan Imam sun warwatsu, sun tarwatse, sun yanke kauna da kuma zama cikin tsoro, babu wani fage na yunkuri na gama-gari a wajen su. Ko da yake a ciki wannan ruwayar Imam Sadiq (AS) yace “Daga a sun dawo sannan kuma suka yi yawa”, wato a hankali a hankali mutane sun dawo da kuma kara yin yawa.

Bayan shahadar Imam Husain (AS) zuwa wani haddi mutane sun razana, to sai dai tsoron bai kai matsayin da zai kawar da tsarin da kungiyar mabiya Ahlulbaiti gaba daya ba. Dalilin hakan kuwa shine cewa hatta lokacin da aka kawo fursinonin yakin karbala a garin Kufa, ana iya ganin wani yunkuri da aka yi wanda ke tabbatar da kasantuwar kungiyar yan Shia.

Ko da yake yayin da muke magana kan kungiyar boye ta yan shi’a ba muna nufin irin kungiyar da a halin yanzu ake gani ba ne; face dai abin nufi shine alaka ta akida da take hada mutane da junan su da kuma sanya su yin sadaukarwa da kuma gudanar da wasu ayyuka a boye. A takaice ana nufin wata al’umma da kwakwalwar mutum zai iya yin tunani, misali a daya daga cikin dararen ranaku da zuriyar Annabi (SAWA) suke a garin Kufa a tsare, wani mutum ya wurga dutse a cikin gidan yarin da ake tsare da su, a lokacin da suka daga dutsen sai suka ga an kulle wata takarda a jikin sa, a cikin takardar an rubuta cewa “gwamnan Kufa ya aike da wani mutum zuwa wajen Yazid a Sham don neman bayanin yadda zai yi da ku. Idan har zuwa daren gobe kuka ji ana kabbara to ku san cewa a wajen za’a kashe ku, idan kuwa baku ji haka ba to ku san cewa yanayi zai yi kyau.

Yayin da muka ji wannan kissar da kyau zamu fahimci cewa wani daga cikin mabiya da kuma yan wannan kungiya ta yan shi’a ne da ke cikin gwamnatin Ibn Ziyad sannan kuma yake da labarin abin da aka kulla da kuma alaka da wannan gidan yarin yake sanar da fursinonin abinda aka tsara ta hanyar kabbara. A wani misali kuma na daban shine Abdullah Bin Afif Azdi wanda ya kasance makaho ne a daidai lokacin da fursinonin yaki suka shigo Kufa yayi wani yunkuri wanda yayi sandaiyyar shahadar sa, akwai irin wadannan mutane a Sham da Kufa wadanda a lokacin da suka ga fursinonin yaki sun nuna musu so da kaunar su, ko dai ta hanyar kuka ko dai ta nuna juyayi ga junan su. Irin hakan ma ya faru a fadar Yazid haka nan a fadar Ibn Ziyad ma.

A saboda haka duk da irin tsoro da fargaba mai tsanani da ta kunno kai bayan abinda ya faru a Karbala to amma lamarin ba shine cewa tsari da kungiyar mabiya Ahlulbaiti ta wargaje da taewatsewa gaba daya bane, face dai bayan gushewar lokaci an samu wasu yunkuri da suka kara irin wannan yanayi na dirar mikiya. Daga nan ne zamu iya fahimtar wannan hadisi na “Mutane sun yi ridda bayan (shahadar) Husain”

 

Zamu cigaba…

SHARE:
Raruwar Magabata 0 Replies to “Yanayin Zamantakewa Da Siyasa Bayan Karbala”