Ahlul Baiti

Jaridar Isar da Sakon Jikokin Manzon Allah (S.A.W)

September 26, 2021

Yanayin Zamantakewa Da Siyasa Bayan Karbala

Cigaba daga rubutun da ya gabata…

SHAHADAR MUKTAR

Lamari na gaba wanda ya taimaka wurin firgitawa da kuma raunana ‘yan shi’a shine lamarin shahadar Muktar a Kufa da ikon da Abdulmalik Bn Marwan ya samu a dukkanin duniyar musulmi. Bayan mutuwar Yazid, daya daga cikin halifofin da suka zo bayan sa shine Mu’awiya Bn Yazid wanda bai yi mulki na sama da watanni 3 ba, bayansa kuma sai Marwan Bn Hakam yazo wanda yayi halifanci na shekaru 2 ko ma kasa sa hakan, bayan sa kuma sai Abdulmalik ya dare karagar mulki wanda ya kasance daga cikin mafi tsari da makircin halifofin Banu Umayya. Dangane da shi ana fadin cewa “Abdulmalik ya kasance mafi tsananin su sannan wanda ya fisu tsari na gudanarwa”.

Abdulmalik ya samu nasarar mallake dukkan duniyar musulmi da sanya ta karkashin ikon sa, inda ya kafa wata hukuma wacce ta yi kaurin suna wajen firgita mutane da kuma amfani da karfi a kan su. Tabbatar da ikon da Abdulmalik ya dogara ne da kawar da dukkan abokan hamayyar sa, Muktar wanda ya kasance alama ta shi’anci tun kafin darewar Abdulmalik karagar mulki Mus’ab Bn Zubair ya kawar da shi.

To amma duk da haka Abdulmalik ya cigaba da kokari wajen ganin bayan wannan yunkuri ba muktar da sauran su na daga kungiyoyi da yunkuri na shi’anci.

A hakikanin gaskiya shi’anci a Iraqi musamman a garin Kufa wanda a lokacin ta kasance daga cikin cibiyoyi na asali na yan shi’a yayi rauni (Sakamakon irin zaluncin da Abdulmalik yake yi wa yan shi’a).

Duk da cewa yunkurin Tawwabun da ya faru a shekara ta 64 da 65 don kuwa a zahiri shahadar Tawwabun ta faru ne a shekara ta 65 ya sama wa yan shi’a wani sabon numfashi a irin yanayi na tsanani da suke ciki a Iraqi, to amma shahadar su ta sake haifar da fargaba da karin dirar mikiya kan yan shi’a a Kufa da kuma Iraqi baki daya.

Haka nan kuma bayan da masu adawa da hukumar umayyawa wato Muktar da Mus’ab Bn Zubair suka fada wa junan su da yaki sannan kuma Abdullahi Zubair daga Makka ya gagara hakuri da Muktar, lamarin da yayi sandaiyyar da Mus’ab ya kashe Muktar, hakan ya sake kara irin wannan fargaba da kuma rage fatan da ake da shi. Daga karshe a lokacin da Abdulmalik ya dare karagar mulki bayan dan wani lokaci ya samu damar mai da dukkan duniyar musulmi karkashin ikon Banu Umayya inda yayi mulki da dukkan karfin sa na tsawon shekaru 21.

Ala kulli haal wannan abubuwa sun faru ne daga musibar Ashura da wasu lammura da suka biyo baya irin su yakin Al-harrah da murkushe yunkirin Tawwabun a iraqi da shahadar Muktar da shahadar Ibrahim Bn Malikul Ashtar Al-Nakha’i da sauran manyan yan shi’a.
Daga karshe dai mabiya Imamai (AS) sun kasance cikin wani yanayi na bakunci da buya.

 

A biyo mu a rubutu na gaba…

SHARE:
Raruwar Magabata One Reply to “Yanayin Zamantakewa Da Siyasa Bayan Karbala”
Ahlul Baiti
Ahlul Baiti

COMMENTS

One comment on “Yanayin Zamantakewa Da Siyasa Bayan Karbala

    Author’s gravatar

    Lallai muna murna da dawowar jaridar mu mai farin jini, Allah Jallat Aza Matuhu ya dafa mana kuma ya qarawa jagorar tafiyar lafiya da wadata wato Maulana Hujjatul Islam Wal muslimin Muhammad Nurr Dass(h) da sauran mataimakan sa Amin!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *