September 25, 2021

Yanayin Zamantakewa Da Siyasa Bayan Karbala (2)

Cigaba daga rubutun da ya gabata…

Tsawon wannan yan shekaru kafin wannan lamari mai muhimmanci ya faru, yan shi’a sun dawo cikin aiyukan su da kuma kokarin dawo da tsarin da suke da shi. Anan Dabari ya nakalto cewa “Mutane sun cigaba da tattaro kayayyakin yaki da shirin yaki”, wato ya.

Shi’a sun kasance suna tara makamai da kuma shirya kansu saboda yaki, a boye suna kiran mutane yan shi’a da wadanda ba yan shi’a ba zuwa ga yunkuri don daukar fansar jinin Husain bn Ali (AS) sannan kuma-kungiya kungiya ta mutane suna amsa musu, wannan yanayi ya cigaba da wanzuwa har zuwa lokacin da Yazid bn Mu’awiya ya mutu.
A saboda haka duk da cewa amfani da karfi da tursasawa sun yi yawa, amma duk da haka ana gudanar da irin wadannan aiyukan kamar yadda Dabari ya nakalto, mai yiwuwa saboda haka ne marubuciyar littafin nan na “Jihadish Shi’a” duk da cewa ba shi’a ba ce sannan kuna bata da wata mahanga ta hakika dangane da Imam Sajjad, to amma ta fahimci wata hakika wadda itace fadin cewa “Yan Shi’a bayan shahadar Imam Husain sun bayyanar da kan su a matsayin wata kungiya mai tsari wadanda akida da alaka ta siyasa ta hada su, kamar yadda kuma suna gudanar da tarurruka da shugabanci, haka nan kuma suna da sojoji. Kungiyar Tawwabun itace alama ta farko ta irin wannan kungiyar”.
A saboda haka duk da cewa wannan kungiya ta yi rauni bayan lamarin Ashura, muna jin cewa yunkurin shi’a ya cigaba da kuma komawa ga yanayin sa na farko wanda haka ne ya haifar da lamarin Al-harrah. A gani na kisan kiyashin Al-harrah wani lokaci ne mai girman gaske cikin tarihin shi’anci wanda ya cutar da mahukamtan lokacin.

Yakin Al-harrah ya faru ne a shekara ta 63 (hijiriyya), a takaice abinda ya faru shine a shekara ta 62 (H) wani matashi marar kwarewa daga Banu Umayya ya zamanto gwamna a Madina wato Usman Bn Muhammad Bn Abi Sufyan. a kokarin sa na janyo hankulan yan shi’an madina sai yayi tunanin cewa zai yi kyau ya gayyaci wasu daga cikin su sukaiwa Yazid ziyara. Don haka sai ya gayyaci wasu daga cikin shugabannin musulmi da wasu daga cikin sahabbai da manyan garin Madina wadanda mafi yawan su masu kaunar Imam Sajjad (AS) ne zuwa birnin Sham don ganawa da Yazid da kuma rage irin sabanin da ake da shi. Sun tafi Sham inda suka gana da Yazid, inda suka cigaba da zama a wajen na tsawon kwanaki, daga nan sai Yazid ya bawa kowanne guda daga cikin su wasu makudan kudade da suka kama daga Dirhami dubu 50 zuwa Dirhami dubu 100 sai suka dawo Madina, a lokacin da suka isa Madina da yake sun ga irin lalatar da ake yi a fadar Yazid din don haka sai suka fara sukar Yazid akasin abin da ake so. Maimakon su zo suna yabon Yazid sai suka koma suna sanar da mutane irin danyen aikin sa, suna ce musu ta yaya za’ayi Yazid ya zama halifa alhali mashayin giya ne, mai wasa da karnuka ne, mai aikata nau’o’i daban-daban na fasikanci da fajirci ne don haka mun tsige shi daga halifanci. Abdullahi Bn Hanzala wanda ya kasance daga cikin manyan mutanen Madina shine ya kirayi mutane da su yunkura wajen kawar da Yazid da kuma yi mishi (Abdullahi Bn Hanzala) mubaya’a.

Wannan yunkurin ne ya sanya Yazid daukan mataki inda ya tura daya daga cikin manyan kwamandojin Banu Umayya mai suna Muslim Bn Uqba tare da wata runduna zuwa Madina don murkushe wannan bore na mutanen Madina. Muslim Bn Uqba ya tafi Madina inda ya killace garin na Madina na tsawon wasu ranaku da nufin murkushe wannan wutar, daga nan sai ya shiga cikin garin, sakamakon irin zubar da jini da danyen aikin da yayi a wannan garin ne ya sanya ake kiran sa da Musrif (Wato mutum mai wuce gona da iri cikin aikin sa) don haka ake ce masa Musrif Bn Uqba.

Abinda ya faru a wannan lamarin na Al-harrah yana da yawan gaske, lamarin ya kasance babban hanyar da aka bi wurin firgita mabiya da masoya Ahlulbaiti (AS) musamman a garin Madina, inda wasu suka gudu wasu kuma aka kashe su, wasu daga cikin mabiya Ahlulbaiti irin su Abdullahi Bn Hanzala da sauran su sukayi Shahada. Labarin hakan ya yadu cikin duniyar musulmi da nuna cewa lalle gwamnatin ba’a shirye take ba ta amince da wani bore.

SHARE:
Raruwar Magabata 0 Replies to “Yanayin Zamantakewa Da Siyasa Bayan Karbala (2)”