September 12, 2021

Yan Sumoga Sun Kashe Jami’in Kwastam A Ogun

Daga Balarabe Idriss

 

Wasu da ake zargin yan Sumoga ne sun hallaka jami’in kwastam har lahira a unguwar Owode dake karamar hukumar Yewa ta Kudu a jahar Ogun a daren jiya Asabar.

Jami’in dai yakasance mai mukamin “Kwastam Asistan”. Rahoto ya nuna cewa an kashe shi ne yayi aiki bayan da suka kama wasu motoci guda biyu zuwa legas, motoci dai an yi sumogan shinkafar kasar waje dasu ne.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar Kwastam a FOU yankin z”Zone A” a garin legas mai suna Theophilus Duniya ya tabbatar da faruwar lamarin duk da ya boye sanayyar ma’aikacin da aka kashe din.

Ya bayyana cewa bayan da jami’an suka kama motocin sun dauke su ne zuwa wani wuri daban amma daya daga cikin motocin biyu sai ta lalace a hanya inda aka tsaya gyaran ta.

A tsaka da gyaran motar ne yan sumogan suka yi ma jami’an dirar ba zata dauke da muggan makamai inda anan ne suka kashe jami’in.

Ya kuma bayyana cewa gawar jami’in an dauke ta zuwa warin ajiyar gawa (mutuware).

Kana ya kara da cewa shugaban Kwastam na yankin yayi Allah waisai da kisan kuma ya umarci binciken gaggawa kan lamarin. Ya kuma ce kwacen kayayyakin da aka haramta shigo dasu kasa zai cigaba babu fashi kuma kama masu wannan aiki yanzu suka fara har sai in sun sauye wannan muguwar ta’ada.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Yan Sumoga Sun Kashe Jami’in Kwastam A Ogun”