November 28, 2022

Yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sanya kwalla, bayan da magoya bayan kwallon kafa suka kai musu hari a tsakiyar Brussels jiya.

‘Yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sanya kwalla, bayan da magoya bayan kwallon kafa suka kai musu hari a tsakiyar Brussels jiya, bayan da kasar Morocco ta lallasa Belgium da ci 2-0 a gasar cin kofin duniya dake gudana a Qatar.
Magoya baya da dama sun farfasa tagogin kantuna, tare da jefa kayan wuta da kona motoci.
Tun kafin a kammala wasan, jama’a da dama, ciki har da wadanda suka rufe fuskokinsu, sun nemi yin arangama da ‘yan sanda, lamarin da ya yi illa ga tsaron jama’a, kamar yadda ‘yan sandan Brussels din suka bayyana a cikin wata sanarwa.
Mai magana da yawun ‘yan sandan ta ce, wasu magoya bayan na dauke da sanduna, haka wani dan jarida ya ji rauni a fuska sanadiyar wasan wuta”.

©Cri(Ibrahim)

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sanya kwalla, bayan da magoya bayan kwallon kafa suka kai musu hari a tsakiyar Brussels jiya.”