September 12, 2021

Yan Sanda Sun Kashe Wani Kwamandan “IPOB” A Jahar Imo

Daga Muhammad Bakir

 

Hukumar yan sanda ta jahar Imo ta bayyana cewa ta kai hari a sansanin masu rajin kafa kasar Biafra inda ta samu nasarar hallaka shugaban sansanin da kuma wasu mutum biyu daga yan ta da kayar bayan.

 

Jami’in hulda da jama’a na hukumar yan sandan jahar CSP Michael Abattam ya bayyana cewa nasarar tasu ta biyo bayan yunkurin hukumar tasu na share bata gari da masu mayan laifuka a jahar.

Jami’in ya bayyana cewa rahotanni ya same su cewa yan kungiyar ta IPOB sun ya da zango a wani kango inda suke shirye shiryen kai hare hare kan yan sanda da kuma ta da zaune tsaye kan nadin sabon gwamna bayan gudanar da zabe a jahar a yan kwanakin nan.

Ya kuma kara da cewa a ranar 11/09/2021 Kungiyar tasu ta kaddamar da farmaki kan yan kungiyar ta IPOB wadanda ke boye a wani kango dake yankin Ngbuka dake karamar hukumar Amaofeke Orlu dake jahar ta Imo.

Isar jami’an tsaron ke da wuya sai yan kungiyar ta IPOB suka bude wuta a jami’an tsaron inda take musayar wuta ta fara aikuwa tsakanin bangarorin biyu.

A yayin musayar wutan, uku daga cikinsu suka rasa rayukan su, daga cikin su akwai Chidera Nnabuhe wanda ake kira Dragon wanda kuma dan ainihin karamar hukumar Orlu kuma ya kasance shugaba a wannan sanansanin a tare dashi akwai J.J da kuma Dadawa su kuwa guda biyun yan asalin Ohazara ne dake jahar Ebonyi.

Ya kuma kara da cewa sun damke wasu guda biyu a raye, cikinsu akwai Emeka Sunday Dan shekara 20 da kuma Anthony Okeke dan shekara 44, ta kuma ce wasu sun tsere cikin daji amma da raunukan harsasai.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Yan Sanda Sun Kashe Wani Kwamandan “IPOB” A Jahar Imo”