November 18, 2022

Yan Sanda sun kama mutane uku da ake zargin sun karbi kudin fansa Naira miliyan 2 da dubu 500 a Zamfara.

Wasu mutane uku da ake zargin sun karbi kudin fansa Naira miliyan 2 da dubu 500 bayan kashe wani yaro dan shekara shida da suka yi garkuwa da shi, jami’an ƴan sandan jihar Zamfara sun kama su.

Mohammed Shehu, jami’in hulda da jama’a na rundunar ƴan sandan ne ya sanar da hakan.

Da yake jawabi ga manema labarai a Gusau. Ya ce, wadanda ake zargin – Kabiru Idi, Danhauwa Kalla da Majami Iliya, sun yi garkuwa da Laminu Sani dan shekaru shida a unguwar Bulunku a cikin garin Gusau inda suka bukaci a biya su kudin fansa.

Kakakin rundunar ƴan sandan ya ce “A ranar 3 ga Nuwamba, 2022, jami’an ‘yan sanda sun kama wadanda ake zargi da laifin yin garkuwa da wani yaro dan shekara shida, Laminu Sani na unguwar Bulunku a Gusau.

“Kamen nasu ya biyo bayan korafin da wani Sani Garba ya kai wa ƴan sanda cewa daya daga cikin wadanda ake zargin mai suna Kabiru Idi na kauyen Yarkatsina a karamar hukumar Bungudu ya yi hayar daki a gidansa kuma ya zauna na tsawon watanni uku.

A lokacin zamansa a gidan ya hada baki da abokan aikinsa suka yi garkuwa da yaron Garba, Laminu, da nufin karbar kudin fansa a wurin mahaifinsa.

An ba su kudi Naira miliyan 2 da dubu 500, ba tare da sanin cewa sun riga sun kashe yaron da aka sace ba.

“A yayin da ake gudanar da bincike, dukkan wadanda ake zargin sun amsa laifin da ake zarginsu da aikatawa tare da bayyana irin rawar da suka taka wajen sace yaron.”

Shehu ya ce nan ba da jimawa ba za a gurfanar da wadanda aka kashen a gaban kotu domin a yi musu shari’a.

© Fadeelah Omar Abdulmalik
#jaridaradio 17/11/2022

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Yan Sanda sun kama mutane uku da ake zargin sun karbi kudin fansa Naira miliyan 2 da dubu 500 a Zamfara.”