September 16, 2021

Yan Sanda Sun Cafke Makasan ‘Dan Sanata Na’Allah

Daga Balarabe Idriss

 

Bayan yan satukai da kisan kisan Abdulkareem Na’Allah dan shekau 36 kuma daya daga cikin yayan Sanata Na’Allah, yan sanda sun damke wasu mutane biyu da ake zargin suna da sa hannu a kisan sa. Rahotanni sun bayyana cewa wadanda ake zargin an kama su ne yan kwanaki kadan da suka gabata.

 

A ranar 29 ga watan Agustan wannan shekarar ne aka tsinci gawar babban dan Sanata Na’Allah a dakin sa a unguwar Malali GRA dake garin Kaduna.

 

Babu gamsassun bayanai kan wadanda aka kama din amma mun samu labarin cewa dukkan su matasa ne yan shekaru 20 da, kana rahoton ya nuna cewa an samu abun hawan su a iyan Jihar.

 

Hukumar yan sandan jahar ta hanyar mai magana da yawun ta ASP Jagile Mohammed ya tabbatar da damke wadanda suka aikata laifin, inda ya shaidawa manema labarai cewa sun kama mutum biyu wanda yanzu haka suna chaji ofis din su.
Shi dai mamacin ya kasance da ga Sanata mai wakiltan Kebbi ta Kudu.

 

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Yan Sanda Sun Cafke Makasan ‘Dan Sanata Na’Allah”