February 20, 2023

Yan Sanda A Zamfara Sun Kama Mutumin Da Ya Sace Mahaifiyarsa

Yayin da rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ke ci gaba da dagewa wajen samar da muhallin da za a tabbatar da sahihin zabe, jami’an ta sun kama wasu mutane takwas da suka hada da wata mata da take kai wa ‘yan Ta’adda bindiga.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, SP Muhammad Shehu ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar rundunar da ke Unguwar Gwaza, Gusau babban birnin jihar.

Ya ce aikin na hadin gwiwa ne da sauran jami’an tsaro a Jihar

SP Shehu ya bayyana cewa, rundunar ta kama wasu masu garkuwa da mutane guda shida da suka hada da wanda ya shirya garkuwa da mahaifiyarsa, aka kuma karbi naira miliyan talatin a matsayin kudin fansa.

A cewar shi, dukkan wadanda ake zargin sun fito ne daga jihar Kaduna wadanda suka hada da Thoms Ya’u, Abdulsamad Mohammed, Bello Abdullahi, Abubakar Namadi, Suleman Gabriel, da Christopher Gabriel.

Ya kara da cewa, bisa bayanan sirri, rundunar ‘yan sandan ta kai samame ga wasu masu garkuwa da mutane guda 6 da suka addabi kauyuka daban-daban a Kaduna, Kano da sauran jihohin da ke makwabtaka da su kamar Zamfara, Sokoto da Katsina.

Daya daga cikin wadanda ake zargin, Thomas Ya’u, ya amsa cewa, a wasu lokutan a shekarar da ta gabata, ya shirya yin garkuwa da mahaifiyarsa da wasu mutane uku, inda suka karbi kudi har Naira miliyan talatin a matsayin kudin fansa

Hakazalika, rundunar ta kuma kama wata mata da ta kware wajen samar da makamai ga ‘yan bindiga da sauran masu aikata laifuka a Zamfara da sauran jihohin da ke makwabtaka da ita.

An kama wacce ake zargin Fatima Sani Kauran Namoda da harsashin bingida kirar AK 46 har guda 323 tun daga garin Lafia dake jihar Nassarawa zuwa ga wani kasurgumin sarkin ‘yan fashi da ya addabi dajin Zamfara.

A cewarta, ta dade tana wannan sana’ar, kuma a baya ta baiwa ‘yan bindigar da ke Zamfara Bindigogi kirar AK 47 guda 3 da kuma harsasai 1000.

Kakakin rundunar ‘yan sandan ya kuma bayyana cewa, an kama wani Rabiu Umar da ke dauke da katin layin waya wato Sim, har sama da 1,000.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Yan Sanda A Zamfara Sun Kama Mutumin Da Ya Sace Mahaifiyarsa”