March 20, 2023

Yan sanda 2 sun mutu a wata arangama tsakanin Sojoji da ‘yan sanda a Jalingo

 

An kashe ‘yan sanda biyu tare da jikkata wasu biyu a wata arangama da aka yi tsakanin sojoji da ‘yan sanda a Jalingo, babban birnin jihar Taraba a ranar Litinin.

Lamarin ya faru ne sakamakon wata ‘yar rashin jituwa tsakanin Sojoji da ‘yan sandan da ke gadin hedikwatar INEC, wanda ya yi sanadin harbe-harbe na sama da mintuna arba’in.

Aminiya ta samu labarin cewa Sojojin sun kuma kai farmaki ofishin ‘yan sandan da ke kusa da hedkwatar INEC inda suka fatattaki ‘yan sandan da ke bakin aiki.

Hakazalika, wasu motoci guda uku da aka ajiye a cikin hedikwatar ‘yan sandan, Sojoji sun lalata su.

Sai dai Kwamishinan ‘yan sanda a jihar, Suleiman Amodu ya ce a yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa, za a kafa babban kwamitin binciken tarnakin domin gano musabbabin faruwar lamarin kuma za a hukunta masu hannu a ciki.

Taron manema labarai na hadin gwiwa ya samu halartar Kwamandan Rundunar Sojin Kasa da ke Jalingo, Birgediya-Janar Frank Etim da Daraktan DSS na jiha.

Sun bayyana lamarin a matsayin abin takaici, sannan sun bukaci mazauna Jalingo da su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum domin an shawo kan lamarin.

A halin da ake ciki dai al’amura sun koma yadda suke a Jalingo, yayin da ababen hawa ke ci gaba da gilmawa a kan tituna kuma wasu shaguna kadan sun bude suna harkokinsu na kasuwanci.

Sai dai har kawo yanzu, hanyoyin da ke kai wa zuwa barikin sojojin a Jalingo na rufe.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Yan sanda 2 sun mutu a wata arangama tsakanin Sojoji da ‘yan sanda a Jalingo”