’Yan Majalisar Dokokin Amurka 14 Sun Yi Kira Kan Sauyin Manufofi Game Da Gwamnatin Isra’ila.

Wasu gungun ‘yan jam’iyyar Democrat a majalisar dokokin Amurka sun bukaci shugaba Joe Biden da ya sauya manufofin Washington game da Falasdinu da Isra’ila tare da gudanar da bincike kan amfani da makaman Amurka da gwamnatin sahyoniya ta yi.
A cewar gidan talabijin na Aljazeera, wakilai goma sha hudu a wata wasika da suka aike wa sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken a ranar Alhamis din da ta gabata, sun jaddada cewa dole ne gwamnatin Biden ta binciki batun amfani da makaman Amurka da Isra’ila take yi wajen take hakkin Falasdinawa.
Sun kuma bukaci gwamnatin Biden ta tabbatar da cewa “ba a kashe kudaden masu jefa kuri’a na Amurkawa kan ayyukan ba sa bisa ka’ida.”
Muna roƙon gwamnatin ku da ta ƙarfafa hanyoyin bin diddigin kuɗi da sa ido don tabbatar da cewa ba a yi amfani da duk taimakon da kasashen waje za su ba Isra’ila a nan gaba ba, gami da makamai da kayan aiki, don tallafawa gallazawar take yi wa haƙƙin ɗan adam, in ji wasiƙar.
Wakilai Jamal Bauman da Sanata Bernie Sanders na daga cikin manyan wadanda suka rattaba hannu kan wasikar, wanda kuma ta bukaci Majalisar ta takaita taimakon dala biliyan 3.8 na taimakon soji da Amurka ke baiwa Isra’ila duk shekara.
Beth Miller, darektan siyasa ta kungiyar “Yahudawa Voice for Peace Action”, da ke goyon bayan ‘yancin Falasdinawa, ta shaida wa Al Jazeera cewa: “Wasikar wadannan ‘yan majalisa goma sha hudu na nuna irin yadda aka samu sauyin ra’ayoyi tsakanin ‘yan Democrat a Amurka.”
Ta kara da cewa: Amurkawa na son kawo karshen goyon bayan da Amurka ke ba wa Isra’ila, wanda a fili take yin amfani da hakan domin cutar da Falasdinawa.