September 26, 2021

‘Yan Boko Haram Sun Kai Hari Wani Gari A Jahar Yobe

Daga Balarabe Idriss


Wasu yan bindiga da ake kyautata zaton yan Boko Haram ne sun farmaki garin Babban-Gida wacce ta kasance helkwatar karamar hukumar Tarmuwa da ke jahar Yobe.

Zuwa yanzu babu cikakkun bayanai kan yadda lamarin ya faru, amma rahoto ya bayyana cewa mayakan na Boko Haram sun yi musayar wuta da jami’an tsaro na tsawon wani lokaci.

Kana mun samu rahoton yadda wasu mazauna garin suka bazama cikin kauyuka da dazuka don neman tseratar da rayukan su.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “‘Yan Boko Haram Sun Kai Hari Wani Gari A Jahar Yobe”